Ko haramta amsar sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati ya dace?4
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka: Bai dace […]
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka:
Bai dace a haramta ba su sarautun ba – Malama Lantana
Malama Lantana Lawal: “Bai wa ma’aikatan gwamnati sarautar gargajiya ta abu ne mai kyau saboda cancanta da kima da kuma daraja take sa wa a bai wa mutum sarauta. Duk wanda ya cancanci sarauta aka ba shi, ashe koda ya bar aikin gwamnatin zai iya shugabantar al’ummar garinsu ko kauyensu. Duk mutumin da ya kai wani matsayi har aka ba shi sarauta, ka ga ai ba talaka ba ne saboda haka idan ya yi ritaya daga aiki ya koma gida sai kawai ya ci gaba da mulki tun da mai mulki ba talaka ba ne.”