Ko haramta amsar sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati ya dace?5
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka: Samar da […]
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka:
Samar da dokar bai dace ba
– Hassan Muhammad
Hassan Muhammad Zurmi: “Abin da ya sa na ce bai dace ba shi ne, ana ba da wadannan sarautu ne saboda a farfado da wadannan mukamai, domin idan ka tambayi wani ba zai gaya maka abin da ake nufi da wasu mukaman ba. Kamar a ce dan Makwayo ko Shantali da sauransu, amma abin da ya dace a yi shi ne kwaskwarima, domin yadda ake ba da abin ba ana ba da wa ba ne bisa cancanta. Misali, idan za a ba da sarautar Sardauna ga wani, to ya dace a duba ko wanda za a ba yana da hali irin na Sardauna? Kuma kamar za a ba wani sarautar Garkuwa, to a duba ko shi wanda za a ba wannan sarautar zai iya kare wannan al’ummar? Kuma abin bakin ciki shi ne, yadda wasu ke ba da sarautar kara zube kuma wasu sai sun kashe kudi ko mu ce sai sun sayi sarautar ake ba su.”