Ko haramta shigo da shinkafa ta hanyoyin kasa ya dace?

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta haramta shigo da shinkafa zuwa kasar nan ta hanyoyin kasa (land borders). Abin tambaya a nan shi ne, shin ko daukar wannan mataki ya dace a wannan lokaci kuma shin ko wannan mataki zai taimaki manoman shinkafa da sauran al’ummar na kasar nan? Wakilanmu sun tattauna da mutane […]

Ko haramta shigo da shinkafa ta hanyoyin kasa ya dace?
Ko haramta shigo da shinkafa ta hanyoyin kasa ya dace?

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta haramta shigo da shinkafa zuwa kasar nan ta hanyoyin kasa (land borders). Abin tambaya a nan shi ne, shin ko daukar wannan mataki ya dace a wannan lokaci kuma shin ko wannan mataki zai taimaki manoman shinkafa da sauran al’ummar na kasar nan? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Matakin zai taimaka amma… -Nasiru Ahmad

Nasiru Ahmad Labbo: “Babu shakka matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na haramta shigo da shinkafa ya dace, sai dai kuma bai kamata a ce a wannan lokacin ne aka yanke hukuncin haka ba. Ina ganin da kamata ya yi a bari sai bayan daminar bana, lokacin an dauki matakan kyautata wa manoman shinkafa na gida yadda za su noma wadda za ta wadaci al’ummar kasar nan. Amma yanzu da aka dauki matakin hana shigo da ita kai tsaye ta hanyoyin kasa, abin zai zama mai kuntatawa ga al’umma, domin farashinta zai hau kuma za a samu karancinta. Amma lallai kam ya kamata gwamnati ta maida hankali wajen kyautata wa manoma tare da ba su isasshen bashin noma da inganta masu yanayin noma na zamani. Haka kuma a samar wa ’yan kasuwa yanayi mai kyau, yadda za su kafa kamfanonin cashe shinkafa da gyara ta, yadda tamu ta gida za ta zama ingantatta kuma a same ta cikin farashi mai rahusa. Wadannan matakai su ya kamata a dauka, domin wadata kasa da abinci da kuma sama wa al’umma abin yi.”

Matakin bai dace ba a yanzu – Bilkisu Yusuf Ali

Bilkisu Yusuf Ali: “Batun gaskiya matakin haramta shigo da shinkafa ta hanyoyin kasa da Gwamnatin Tarayya ta dauka a wannan lokaci bai dace ba, domin kuwa matakin zai haddasa tashin farashin shinkafa a yanzu, sannan kuma hakan zai haifar da kunci ga al’ummar kasar nan. Matakin kuma zai takura wa ’yan kasuwa da suka saka dukiyarsu suka sayo shinkafar nan, kafin su shigo da ita kuma aka haramta. Wannan zai sanya su kasance cikin matsala da asara. Ni a ganina, da kamata ya yi a karfafa wa manomanmu na gida tukunna, su samu jari mai karfi, su noma isassar shinkafar da za ta wadaci kasar nan, daga nan sai a sanya wannan doka. Idan an yi haka, farashin shinkafar zai yi kasa, manomanmu kuma za su samu riba, ’yan kasuwarmu kuma su amfana.”

daukar matakin da sauran lokaci – Muhammad Ibrahim

Alhaji Muhammad Ibrahim sakatare: “Ni a ganina da kuma irin fahimtar da na yi wa wannan shiri na Gwamntin Tarayya game da batun aiki ko daukar wata dokar ta hana shigowa da shinkafa ko kuma abinci a kasar nan, a gaskiya zan iya cewa da sauran lokaci; domin ganin ainihin akasarin manoma a kasar nan talakawa ne, ya ku bayi kuma su masu hannu da shuni mafiya yawansu ba su maida hankali ko su sa himma wajen bunkasar noma da wadata kasa da abinci ballantana a ce a huta da kawo mana daukin abinci daga waje da ya hada da shinkafar da ake magana a kanta.  Don haka, a sanin kowane noma ya fi karfin talaka sai dai idan ainihin ita gwamnatin za ta yi da gaske, ta tashi tsaye wajen tabbatar ta hada hannu da masu kudi domin bunkasar harkar noma da wadata kasa da abinci, kamar yadda manyan kasashen da suka ci gaba suke yi; kafin ta ce ta kafa dokar hana shigo da abinci a kasar nan amma ba a cikin wannan lokaci ba. Don haka dakatar da shigo da duk wani abu mai muhimmanci ga rayuwarmu ba ta taso ba.

daukar matakin bai dace ba – Sani Abdullahi

Malam Sani Abdullahi: “A hakikanin gaskiya, dangane da batun hana shigowa da abinci a kasar nan, musamman shinkafa kamar yadda gwamnatin ta yi, ina ganin rashin amfaninsa ya fi yawa a kan amfanin, idan aka yi la’akari da halin da kasar nan take a ciki na rashin wadatar abinci da sauransu. Don haka ina ganin kafin wannan dokar ta fara aiki, to ya kamata a ce gwamnatin ta nemi shawarwari daga masu hangen nesa kuma masu aiki da ilimin canjin yanayi na rayuwar dan Adam. Kuma kafin komai, gwamnatin ta yi hakuri, ta bari ana shigowa da abincin ta hanyar da doka ta yarda da ita kuma ta ci gaba da tallafa wa manoma marasa karfi da masu karfin. Ta wannan hanyar sai ka ga an samu wadatar abinci, ba sai shinkafar kadai ba. Don haka a bi wannan shirin da hankali, domin muddin aka yi garaje, garin neman ido sai a rasa kai; domin noma ba ya yiwuwa da yunwa kuma masu iya magana suna cewa da ruwan ciki ake jan na rijiya kuma ya kamata a gane cewa wadata kasa da abinci hakki ne da ya rataya a wuyan ita gwamnatin kasa. Kafin komai, ta yi oda a shigo da abinci tare da ci gaba da tallafa wa manoma masu karfi da talakawa.

Matakin ya yi daidai- Muntari Allah-Wahid

Muntari Allah-Wahid: “Bisa ga wadannan dalilai, ina ganin hana shigowa da shinkafar da gwamnati ta yi daga wasu kan iyakokin kasar nan ta yi daidai. Dalilina na farko shi ne, hakika na san mutane na bukatar shinkafar kamar yadda aka saba. To rufe iyakar zai sa manoman kasar su ci gaba da yin noma, ba ma nata ba kadai, za a samu hakakar tattalin arzikin kasa, za a kuma samu ayyukan yi a kasa. Kuma hakan zai sa shinkafar wajen ta yi karanci, wanda hakan zai kawo darajar ta cikin gidan da aka noma. Ke nan baya ga samun ayyukan yi, zai kuma sa mu iya ciyar da kanmu har ma mu ciyar da wasu. Sai mu dubi kasar China a kan batun yawan jama’a amma ita ke ciyar da kanta. Amma sai kullum mu dauki aikin yi muna kai wa wasu kasashe sannan kuma mu dawo mu ce muna son kasa ta ba ’ya’yanmu ko mu kanmu aikin yi? Don haka na goyi bayan wannan shiri na gwamnati.”

Ina goyon bayan matakin – Abban Zamani

Abban Zamani: “Na goyi bayan wannan shiri. Farko ma sai in ce Allah Ya yi wa Shugaban kasa albarka a kan wannan tunani da ya yi. Ai duk kasar da ta dogara da cewa sai wata kasa ta ciyar da ita, to kuwa za a iya shigo mata da abin da za ta karba dole. Ai kamar magidancin da ya bar wani yana ciyar da iyalainsa ne, to sai an wayi gari matar ta koma ga wancan. Saboda haka shugaba ya tsare kasarsa da jama’arsa, don kada a mayar da mu ba yi. Illa dai abin da gwamnati za ta yi a nan shi ne, duk lokacin da za a ba da tallafin noman nan, to ya bi ta hannun masu unguwanni da wakillai, domin su ke tare da jama’a kuma su suka san manoman nan na gaskiya. Amma muddin aka sanya ’yan siyasa a ciki to kuma abin zai lalace ya koma batun siyasa, ba zai yi tasirin da ake so ba. Babban misali a nan shi ne, abin da ya faru a lokacin da aka bullo da shirin noman rogo na Obasanjo.”