Ko hirar aikin mai dakina ba ma yi ballantana na yi mata katsalandan — Sanata Bulkacuwa

Sannan taimako da na ce tana yi, wannan dabi’arta ce, halinta ne.

Ko hirar aikin mai dakina ba ma yi ballantana na yi mata katsalandan — Sanata Bulkacuwa

Tsohon wakilin shiyyar Bauchi ta Arewa a Majalisar Dattawa, Sanata Adamu Bulkacuwa ya musanta fahimtar da aka yi masa na cewa ya taka rawa a wasu hukunce-hukunce da matarsa, Zainab Adam Bulkacuwa ta yanke a lokacin tana Shugabar Kotun Daukaka Kara.

Sanata Bulkacuwa ya ce an yi wa kalamansa bahaguwar fassara a lokacin da ya alakanta aikin matarsa da majalisa.

Sanatan ya yi kalaman ne a zaman karshe na Majalisa ta 9, inda ya yi ikirarin cewa ya yi amfani da matsayinsa wajen nema wa abokansa ’yan majalisa alfarma a wajen matarsa a lokacin da take rike da shugabancin Kotun Daukaka Kara.

A cewarsa tsohon shugaban Majalisar Dattawa ne, Sanata Ahmed Lawal ya yanke masa hanzari inda ya rika masa katsalandan a lokacin da ya ke bayani.

“To ba a ma bar ni na karasa ba, wasu kalmomi kawai da na fara kamar cewa na gode mata, ta yi hakuri da ni, ni ina siyasa ita kuma tana shari’a.

“Sannan taimako da na ce tana yi, wannan dabi’arta ce, halinta ne.

“Ba a ma jira na fadi taimakon wadanne iri ne, don akwai taimako iri sun fi dari, wanda kowane ma’aikaci, ko na shari’a ne ko likita ne ko injiniya ne, kowa zai iya yin taimako a kan aikinsa.

“Taimakon ba wai yana nufin ka karya ka’idar doka ko aikata abinda ba daidai b,” in ji Bulkachuwa.

Sanatan ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi masa na shiga hurumin aikin matarsa [Zainab Adam Bulkacuwa] a lokacin da take aiki.

“Yadda mu ke zama da ita ban taba ce mata ga yadda za ki yi ba, ga yadda za ki yi shari’ar ki, ko yadda za ki yi da ofis dinki ba. Wannan maganar ma ko a gida ba ma yi.”

Sai dai kalaman da ya furta sun janyo wa tsohon sanatan da matarsa, Zainab Bulkachuwa zargi .

Daga ina gizo ya fara saka?

Tun a wani bidiyon da aka nada da ya karade shafukan sada zumunta, ya nuna Sanata Bulkacuwa yana jawabin bankwana a cikin zauren Majalisar Dattawa.

“A cikin zauren nan, ina iya ganin fuskokin da suka zo, suka nemi taimako na lokacin da mata ta take shugabar Kotun Daukaka Kara ta Kasa.”

Sai dai yana cikin bayani ne sai tsohon shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal ya katse masa hanzari tare da yi ma sa hannunka mai sanda.

“Irin wadannan kalamai masu harshen damo za su iya nuna an samu alfarma ko wani abu makamancin haka”, in ji shi Sanata Lawal

A yanzu haka Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA ta aike da wasika a hukumance zuwa ga babban sufeton ’yan sandan kasar, da kuma Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC da EFCC .

Kungiyar ta nemi bangarorin uku da su gudanar da bincike a kan sanatan.

Wasu masu fafituka sun nemi a hada har da matar sa da ya ambata a cikin binciken.