Ko ina kudin sulallan Najeriya suka shige?
Sanin kowa ne a lokutan da suka shude, al’ummomi na tafiyar da harkokin kasuwancinsu ta hanyar dabarar ban gishiri in ba ka manda; wanda hakan kan jawo matsaloli da dama da ke hana ruwa gudu wajen ci gaban kasuwanci da harkokin bunkasa tattalin arziki. Matsalolin da ake fuskanta musamman wajen neman wanda ke bukatar kayanka […]
Sanin kowa ne a lokutan da suka shude, al’ummomi na tafiyar da harkokin kasuwancinsu ta hanyar dabarar ban gishiri in ba ka manda; wanda hakan kan jawo matsaloli da dama da ke hana ruwa gudu wajen ci gaban kasuwanci da harkokin bunkasa tattalin arziki. Matsalolin da ake fuskanta musamman wajen neman wanda ke bukatar kayanka sannan kuma kai ma kana da bukatar irin kayan da ke hannunsa don yin musanya. Yana daga cikin matsalar irin wannan salo na kasuwanci, rashin samun cikakken ma’auni wanda zai zama ba cuta ba cutarwa tsakanin masu musanyar kayayyakin.
Da tafiya ta yi nisa sai aka sami ci gaban amfani da Wuri da wasu karafuna masu daraja, sai dai duk da haka kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, musamman ta wajen samun cikakken ma’aunin darajar kayan.
An samu canji a harkokin cinikayya, lokacin da aka samar da kudi. Kudi ya kasance dukkan wani abu da daukacin jama’ar gari ko kasa suka aminta da shi don gudanar da harkokin kasuwanci na saye da sayarwa, biyan basussuka, tantance darajar kaya da kuma ajiya don amfanin gaba. An kirkiri kudi na takarda da kuma karfuna, wadanda za su ba da damar tafiyar da kasuwanci ba tare da samun wani tasgaro ba, musamman tunda kowanne kaya na da farashi daidai da darajarsa.
A Najeriya, har bayan samun ’yancin kai; an dau lokaci mai tsayi ana amfani da kudin gado; wanda Turawan mulkin mallaka suka gadar wa kasar, kafin daga baya kasar ta samar da kudinta mai suna Naira da Kobo ta kuma daina amfani da Fam da Sulai, wanda kudin kasar Birtaniya ne. An samar da kudin kasa a 1973 kuma akasarin kudin na karfe ne, wato sulalla na rabin Kobo, Kobo 1, Kobo 5, Kobo 10, Kobo 25, Kobo 50 da kuma Kobo 100 wanda ake kiransu da Taro, Kobo, Sisi, Sulai, Biyu da Sisi, Sulai biyar sai Kuma dari ko kuma Naira daya. An fara kirkirar kudin takarda na Naira Ashirin 20 wadda aka fi sani da fam 10 a 1977 don tunawa da tsohon Shugaban kasa Janar Murtala. Haka kuma an fitar da takardun kudi na Naira 1, Naira 5 da Naira 10, wadanda aka sanya hotunan ’yan mazan jiya da suka hada da Herbert Macauley, Sa Abubakar Tafawa balewa da kuma Alban Ikoku. Samar da wadannan kudaden na kasa ya bunkasa harkar kasuwanci da kuma inganta tattalin arzikin kasa; sannan kuma kudin ya samu martaba a kasuwannin duniya, musamman a kasuwar hada-hadar kudade da harkokin cinikayya ta kasashen waje, don kuwa a lokacin da aka samar da kudi a Najeriya, darajar Naira 2 daidai take da fam 1 na Birtaniya, haka kuma darajar kudin ta dara na Amurka da wasu daga manyan kasashen duniya; don a wancan lokacin Naira 1 daidai take da Dalar Amurka 10. An kuma samar da wasu takardun kudin har zuwa yau sannan kuma an canza wa wasu fasali, sai dai a yanzu ba a maganar sulalla a zahiri sai dai a tsarin rubutu, dayake har yanzu suna cikin kudaden da Najeriya ke amfani da su.
A da saboda samuwar kudin sulalla, an sami bunkasar harkar cinikayya, sannan kuma farashin kayan masarufi ya daidaita, gami da samar da sauki wajen auna darajar kaya a kasuwa, a inda ake amfani da sulalla wajen bayar da sauran canji; wanda hakan ba ya samuwa a lokacin cikinin ban gishiri in ba ka manda.
Darajar sulalla ta fara faduwa a kasar nan a 1991, lokacin da aka canza takardar kudin Naira daya da kuma ta Sulai Biyar zuwa kudin karafa. Hakan ya jawo batan kudin sulalla, musamman ganin yadda farashin kayayayyaki har da kayan kwalan da makulashe na yara suka haura darajar kudin sulalla. A wancan lokacin kodayake ina ajin firamare amma nakan tuna yadda ake ba ni kudin tara na makaranta da sulalla, don kuwa ba mu isa a ba mu kudin takarda ba. Haka kuma idan muka tashi tafiya makarantar allo ko islamiyya, akan ba mu sulai biyu da sisi, wanda yake dunkulalle daya kuma mukan yi amfani da shi har ma mu sami ragowar da muke adanawa don amfanin gaba.
Bayan haka kuma bacewar farashin kaya wanda yake alamta kwabbai a kasar nan na daga cikin babban dalilin da ya janyo batan dabon da kudin sulalla suka yi. A da akan samu farashin kayan masarufi kamar irin su omo, sabulu, man shafawa a farashin da dole sai an yi amfani da sulalla wajen cinikayya. Misali, Naira Uku da Kwabo Hamsin (N3.50k) ko kuma kayan Naira Goma sha bakwai da Kwabo 9 (N13.9k). Wannan ka iya tilasta amfani da kananan kudade da suka hada da sulalla kuma su ba da damar gudanar da hada-hadar kanana da matsakaitan kasuwanci a kasar, wanda su ma suna da matukar muhimmanci wajen ci gaban tattalin arzikin kasa. Haka kuma farashin kaya mai rabin kwabo na bunkasa darajar kudi sannan kuma yana habaka tattalin arziki ta hanyoyi da dama.
A da yanayin farashin kaya a Najeriya ya aminta da tsarin amfani darabin kwabo, don kuwa hatta ma’aikatan gwamnati akan biya su albashinsu duka har da kwabbai a sama don kuwa a lokacin ana iya biyan bukata da wadannan kwabban, sabanin yanzu. Abin takaicin a yanzu shi ne, har a bankuna da wajen biyan kudaden haraji koda kuwa lissafi ya nuna rabin kwabban, to sai dai dayanku ya yafe don kuwa ko da an ba ka su to ba za su yi maka amfanin komai ba sai dai a bar ka da dakonsu.
A karshe, tabbas akwai bukatar gwamnati ta dawo da tsarin amfani da kudin sulalla ta hanyar fito da tsabar kudin karfe, kodayake har ila yau a gwamnatance amma a rubuce a takarda ba a zahiri ba sulalla na nan a kasar nan. Duk da yake a tsarin kudaden Najeriya akwai su amma saboda rashin amfani da su ya janyo suka yi batan dabo tun da dadewa don kuwa a yanzu yara ’yan shekara 10 in ka nuna masu kwabo da yawansu ba su san shi ba, don ni na san yaron da aka ba shi kwandalar Naira daya amma yake tambayar babansa kudin wacce kasar ne don bai san shi ba, bai taba ganinsa ba balle ya yi amfani da shi.
Ina kara kira ga gwamnati da hukumomin da ke da ruwa da tsaki wajen samar da kudade a kasa da su dawo da martabar kudin sulalla don saukaka wa jama’a harkokin kasuwanci da cinikayya, wanda na yi imanin yin hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan kuma darajar Naira za ta karu a idon duniya.
Mudassir ya rubuto daga NTA Zariya (08065652808).