Ko jam’iyyar APC za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya?1
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane […]
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kan batun kuma ga abin da suka fada:
Za a iya samun ci gaba – Umaru Muhammad
Malam Umaru Muhammad danbatta: “Ko daga ranar da aka ce an yi wa wannan jam’iyyar rajista, ai an fara samun ci gaba a fuskar siyasar kasar nan, domin kowa ya sani tun a wancan lokaci da kasar nan aka dawo da ita a kan mulkin dimukradiyya a 1999, kawo ranar da Allah Ya taimaki ’yan Najeriya aka yi wa wannan jam’iyya rajista; ’ya’yan jamiyyar PDP suka maida mulkin kasar nan tamkar gadon gidansu ne, sai wanda suke so ne za su dora. Amma da ikon Allah yanzu haka zai kau, domin wannan hada kai da ’ya’yan jam’iyyun adawa suka yi har suka samu fito da jam’iyya guda; wannan ma kadai babban ci gaba ne a siyasar kasar nan.