Ko jam’iyyar APC za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya?2
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane […]
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kan batun kuma ga abin da suka fada:
Za ta canja halayyar ’yan Najeriya – Malam Yakubu
Alhaji Umaru Gosulo Pz. Zariya: “kwarai kuwa, sabuwar jam’iyar APC za ta canza siyasar Najeriya. Dalili a nan shi ne, har in aka ce wannan sabuwa jam’iyya ta APC ta kafa gwamnati, to jama’ar Najeriya gaba daya za su canza daga inda suke, domin yanzu siyasar ta shiga rudani. Hange mutanan da suka kirkire ta dukkansu an san irin jagorancin da suka yi a kasar nan. ACP, tun da ta sami rijista a matsayintana babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, mu mun shiga sabuwar jamhuriya a Najeriya.”