Ko jam’iyyar APC za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya?3
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane […]
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kan batun kuma ga abin da suka fada:
Za ta iya kawo canji – Abban Saudat
Kabiru Ghali Abban Saudat: “Jam’iyyar APC za ta iya kawo canji mai amfani a siyasar Najeriya saboda dalilai kamar haka: Na farko, jama’a sun gama gajiya da mulkin kama-karya na jam’iyyar PDP, wacce ta shekara 15 tana mulki ba ta tsinana wa jama’a komai ba. Na biyu kuma akwai zarata a cikin sabuwar jam’iyyar APC, wadanda kishin al’umma ne kawai a gabansu. Abu na karshe kuma shi ne, kasancewar ita hadakar jam’iyyu ce da yawa, hakan zai sa ta iya kawo sauyi mai amfani, domin an ce hannu da yawa maganin kazamar miya.”