Ko jam’iyyar APC za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya?5
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane […]
Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kan batun kuma ga abin da suka fada:
Ba za ta iya kawo wani canji ba – Malam Sabo Musa
Malam Sabo Musa, Matasa Motors Katsina: “Ni ina ganin bawani canji da da za a samu wanda zai sha bamban da na yanzu saboda ai jama’a sun kasa fahimtar cewa, mafiya yawan ’yan jam’iyyar APC, in ban da Janar Buhari da wasu tsiraru, ai ’yan PDP ne da suka fadi zabe, suka canza sheka. Don haka, ba wata manufa gare su ba kuma shi kansa Buhari ya san ba irin manufarsu daya ba, kawai sun dauke shi a matsayin ‘Tudun Mun Tsira.’ Da sun ci zabe inda suka baro, ba su zuwa inda yake kuma da sun san za su iya cin zabe ba tare da Janar Buhari ba, da ba su bin shi. Don haka mun san kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi, gyauron PDP ne suka hadu suka kafa APC, da zarar ita PDP ta dinke barakarta, ta tsaida ’yantakarar da suka cancanta, za ta ci gaba da zama daram.”