Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 2
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: APC za ta iya karbar mulki – […]
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
APC za ta iya karbar mulki – Auwalu Yahaya
Auwalu Yahaya Yunusa: “Bisa dukkan alamu dai, jam’iyyar APC za ta iya karbar mulki a hannun jam’iyya mai mulki wato PDP; duk da kasancewa suna kurarin iya kwace kujerun gwamnonin da suka ci zabe karkashin jam’iyyar suka koma APC, alhalin sun mance akwai wadanda su ma suka ci zabe a wata jam’iyyar suka dawo PDP. Dalilina na fadin haka kuwa, jama’a sun dawo daga rakiyar mulkin PDP saboda ba ta mulki na adalci kuma ba ta kawo ci gaba a kasa ba, shekara 14 suna mulki. Kullum sai ci baya ake samu. To gara a canja jam’iyyar, wala Allah a samu canji.