Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 3
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Za ta iya kwace mulki – Aminu […]
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Za ta iya kwace mulki – Aminu Abubakar
Aminu Abubakar Kano: “Gaskiya sabuwar jam’iyya za ta iya kayar da jam’iyya mai mulki idan muka yi la’akari da alamun sauya shekar da wasu gwamnonin PDP da ke mulki su biyar din nan duk da barazanar da jam’iyya ke yi musu har ma da kai magana kotu, duk shure-shure ba zai hana mutuwa ba; domin ka ga za su tabbata kowane gwamna ya umarci shugaban karamar hukumarsa da ya tabbata ya kawo kujerar duk dan takarar jam’iyyar APC,