Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 4
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: APC za ta kwace mulki – Nura […]
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
APC za ta kwace mulki – Nura Abubakar
Nura Abubakar: “A ra’ayina, insha Allah APC za ta kwace mulki a hannun PDP a zaben 2015, musamman idan aka yi la’akari da irin rikice-rikicen da PDP ke fama da su a yanzu. A baya, jam’iyar PDP na da gwamnoni 23 ne amma a yanzu saboda rikicinsu gwamnoni biyar sun fice daga jam’iyar. Yanzu PDP na da gwamnoni 18 ne, ita kuma jam’iyar APC na da gwamnoni 16. Ka ga ke nan akwai alamar nasara a APC saboda haka ina ganin abu ne mai sauki APC ta kwace mulki, domin babu wata alama da ke nuna PDP za ta kai labari.”