Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 5
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Zai yiwu APC ta kwace mulki – […]
Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Zai yiwu APC ta kwace mulki – Zubairu Sham’una
Zubairu Sham’una: “Amsar wannan tambayar a bayyane take, musamman ganin samun hadakar jam’iyyu da ba a taba samu ba sai wannan karo. Na biyu, saboda rudani da aka samu a jam’iyyar PDP har ya jawo wasu gwamnoni guda biyar suka shigo cikin wannan hadakar. Kuma ana sa ran biyowar wasu gwamnoni. Haka nan kuma irin fadan da ke kara fitowa fili tsakanin tsohon Shugaban kasa Obasanjo da Jonathan. Duk wannan wasu alamu ne masu karfi, wanda suke nuna cewa mulki ya kubuce wa PDP zuwa hannun APC a zaben 2015, in Allah Ya yarda.”