Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 6

Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:   Alamu sun nuna APC za ta iya […]

Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 6
Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 6

Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

 

Alamu sun nuna APC za ta iya – Hajiya Hajarat
Hajiya Hajarat danyaro Ibrahim: “A ra’ayina dai, idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa tsakanin jam’iyyar APC da ta PDP a kasar nan, ya zame dole jam’iyyar APC ta kada PDP. Kai, jam’iyyar APC ta ma kada PDP za a ce, don idan ka lura ba gwamnonin PDP kadai ba har ma da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wanda daya ne daga cikin masu fada a ji na PDP; a jiyar nan ya aiko wa Shugaba Jonathan wata wasika; inda ya tono asirinsa na mummunan shugabancin kasar nan da yake yi. Ya kuma shawarce shi cewa kada ma ya yi tunanin ya tsaya takara a zabe mai zuwa saboda ko ya tsaya ma za a kada shi.