Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 7

Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Farin jini zai sa APC ta yi nasara […]

Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 7
Ko jam’iyyar APC za ta iya kawar da gwamnati mai ci ta PDP? 7

Ga dukkan alamu jam’iyyar APC ta zama cikakkar jam’iyyar adawa a Najeriya. Sai dai a yayin da zabubbuka ke karatowa, ko jam’iyyar za ta iya kawar da gwamnatin PDP da ke kan mulki tun 1999? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Farin jini zai sa APC ta yi nasara – Ann Dogonyaro

Misis Ann Dogonyaro: “Abin da zan ce game da batun ko sabuwar jam’iyyar APC za ta iya yin nasara a zabubbuka masu zuwa a kasar nan shi ne, ka ga da farko jam’iyyar APC jam’iyya ce da jama’a da dama musamman talakawa a kasar nan sun rungume ta da hannu biyu. Kuma ga irin shirye-shirye da take yi su ma sun nuna cewa lallai za ta samu nasara ta kada PDP. Jama’a suna neman canji don sun gaji da shugabancin PDP. Ga talakawa na fama da wahala, matasa ba aikin yi, mata da yara duk kowa yana fama da wahala.