Ko Jihar Katsina za ta fara ciwo bashi ne?
Kwanakin baya ne ’yan majalisar dokokin Jihar Katsina.suka amince wa Shugaban Majalisar Alhaji Aliyu Sabi’u Muduru damar ya yi amfani da Naira milyan 50.wajen yi wa gidansa da na mataimakinsa kwaskwarima.kafin tafiyar tsohuwar Gwamnati ta Shema.ta yi wa wadannnan gidajen gyaran fuska, amma da yake wannan sabuwar gwamnati ce, sai suka bukaci.a sake gyaran da […]
Kwanakin baya ne ’yan majalisar dokokin Jihar Katsina.suka amince wa Shugaban Majalisar Alhaji Aliyu Sabi’u Muduru damar ya yi amfani da Naira milyan 50.wajen yi wa gidansa da na mataimakinsa kwaskwarima.kafin tafiyar tsohuwar Gwamnati ta Shema.ta yi wa wadannnan gidajen gyaran fuska, amma da yake wannan sabuwar gwamnati ce, sai suka bukaci.a sake gyaran da suka iske.
An bi duk wata doka ta amincewa da kudin wannan aikin,.inda aka gabatar da bukatar aka tattauna, aka kuma amince. Kuma yan majalisar suka sa hannu kamar yadda doka ta tanada.sannan aka fitar da kudin aikin.Naira milyan 50 na yi wa gidajen biyu kwaskwarima. Bayan wannan zama ne. na amincewa da wannan kudi.sai majalisar ta tafi hutu, inda shugaban ya yi tafiya zuwa kasashen ketare. Don ya wartsake daga gajiyar da ke bi masa jiki, .shugaban majalisar ya yi balaguro sosai kafin ya dawo.
Aikin farko da majalisar ta fara yi, bayan dawowarta shi ne.tattaunawa akan neman amincewar da Gwamnan Katsina ya rubuto na zai karbo wani bashi daga wajen Babban Bankin kasa don raba wa jama’a su karfafa kasuwancinsu.
Bashi ne, na sama da Naira dubu biyu, wanda yana da ruwa kuma yana da ka’ida da lokacin mayar da shi. daya daga cikin kaidarsa shine. Gwamnatin jiha ce, za ta zama abin dogaro (guarantor).na amsar shi,. kuma in har aka samu matsala na rashin biya Babban Bankin kasa , zai iya rike kudin jihar har sai ta biya, ko kuma a yi tsarin da zai zame kudinsa kai tsaye.
An ce, ruwan da ke tattare da bashinyana da dan kauri. ‘Yan majalisar sun bi duk doka wadda ta ba su damar bin ka’ida kafin su amince. Kuma suka bi daki –daki, sannan suka bai wa gwamnan amincewrsu na ciwo wannan bashi. Yanzu gwamnatin jihar na da cikakkar doka na amso wannan bashi daga Babban Bankin Najeriya [CBN].
Wannan shi ne Bashi mafi girma da jihar za ta taba ciwowa a tarihin kafuwar tun daga 1987 zuwa yanzu.kuma shi ne bashin farko da jihar za ta ciwo tun da aka dawo mulkin farar hula.Umaru Musa bai ciwo wa jihar bashi ba. [Allah ya jikansa], Shema ma ya yi ikirarin, amma bai ciwo bashi ba. Wannan gwamnatin kafin ta kwana 100 ta fara neman iznin ciwo bashi daga majalisar dokoki.
Abin la‘akari da su a lamarin shine, na farko ba a nemi shawarar jama’a ba don ciwo wannan bashin. Wasu jihohi idan za s yiu irin wannan sai sun nemi ra’ayin wadanda suka zabe su? Tunda da sunan jihar za a ciwo, kuma kudin jihar za a fitar a biya, me yasa wannnan ba a yi haka ba? Hatta zamanin soja ana neman ra’ayin jama’a.kafin a ciwo bashi, Janar Babangida da zai karbo bashin Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) ya nemi jin ra’ayin jama’a. me yasa ba a yi haka ba?
Na biyu, me kuma yasa ba a wayar da kan jama a ba. akan wannan bashin da za a ciwo musu? Labarin kawai suka ji a kafofin watsa labaran jiha. Za a ciwo bashi. Me yasa? Ya akayi? Ba wanda ya sani. Me yasa haka?
Na uku, ance raba wa ’yan kasuwa za a yi wane. ka’ida za a bi don a yi adalcin wajen ganin cewa kudin sun isa inda ya dace? Ya za kafa kwamitocin da za su rabar da su? Su za su zama membobin kwamitocin? Domin akwai rade –radin za a raba wa wasu masu uwa a
gindin murhu ne, kuma gwamnati ta biya musu. Ana cewa wasu ne za su ci bulus, da gumin ’yan jihar baki daya.
Lamari na hudu, shi ne, me yasa ma gwamnatin ta ciwo bashin? ’Yan jihar na bin duk kudin da ake baiwa jihar a wata kamar yadda ake bugawa a jaridu. Wanda a watan da ya gabata. na Yuli. Jihar ta karbi sama da Naira biliyan 14.
Ga kudin da aka raba wa jahohi, ba wanda ya san nawa aka bai wa Katsina, .ga kudin da aka tarar a asusun ajiya daban-daban na jihar, wanda tsohuwar gwamnati ta bari; .me zai sa ba za a ciro daga ajiyar ba; sai a ciwo alhali yana da da ruwa mai kima?
Abu na biyar, tunda har ana tsammanin za a kwato kudi daga hannun tsohon Gwamna Shema .me zai sa ba za a jira sai an karbo ba, sannan a raba wa ’yan kasuwa maimakon a yi gaggawar ciwo bashi.?
Bashin nan , ba a kai ga amso shi ba .izni kawai aka nema a wajen majalisa. Kuma ta bayar da wannan ikon. Abin da ya kamata kafin akai ga karbowa a yi wa jama’a duk bayanin da ya dace, a kuma nemi izninsu. kafin a ciwo musu albasa a bakinsu.
Danjuma Katsina. Dan jarida ne.mazaunin Katsina. 08035904408 email. [email protected].