‘Ko kallon ka ba zan yi ba in ka ce ga aikin gwamnati in bar sayar da dafaffiyar ganda’

Matashin ya ce sana’ar ta gama yi mishi komai a rayuwa.

‘Ko kallon ka ba zan yi ba in ka ce ga aikin gwamnati in bar sayar da dafaffiyar ganda’

Ganda

Sayar da ganda wato dafaffun kafafun dabbobi da fatunsu dadadden kasuwanci ne da ke da alaka da harkar fawa. Aminiya ta zanta da wani matashi da ke sayar da ganda a Katsina mai suna Aminu Abdulmumin wanda ya ce akwai rufin rufin asiri a wannan kasuwanci:

Yaya ka fara sayar da ganda wato dafaffen kai da kafafu da fatar dabbobi?

To farko sunana Aminu Abdulmuminu wanda aka sani da Aminu Mai-Kanu Bakin Kasuwa, Katsina. Sayar da dafaffen kan awaki da tumaki da raguna da shanu shi ne kasuwancin da nake yi kuma na gada ne daga mahaifina.

In muka gyara kafin mu dafa mutum ya ce yana son danyen, mukan sayar masa, amma na fi sayar da dafaffe.Tun mahaifina yana ja na ina ki, ka san sha’anin yarinta har na fara tsayawa. Yau in ya nuna mani wannan sashen gobe wancan bangaren zai nuna mani.

To ga shi ni ke gudanar da shi da kaina, kuma ya fara sakar mani komai kafin ya bar duniya, Allah Ya jikansa da rahama.

Ko akwai wani abu da kake bukata kafin a fito wajen sayarwa?

To farko ka ga shi kan da za a dafa in ba mu samu a nan cikin gari ba mukan tafi kasuwannin kauye. Sannan a yi cefane da kayan yaji, sai wukar yankawa da farantai ko abubuwan zubawa. Wadansu sukan hada da waina (masa) ko doya, ni ina hadawa da waina.

Sannan ba na mutum guda ba ne. Akwai masu babbaka da gyarawa da masu dafawa, sannan wurin sayarwa dole a samu masu taimakawa. A nan tare nake da yayana Abubakar muna sayarwa, sai yara masu wanke kayan da muke amfani da su don zuba wa jama’a.

Daga fara wannan kasuwanci me ka samu da ita?

To gaskiya tunda mahaifina ya rasu, ni nake kula da hidimar gidanmu kuma duk wani rufin asiri da muke nema, to sayar da ganda tana dauke da shi. Yanzu ka ce mani ga aikin gwamnati ko na kamfani in bar kasuwancin ganda ko kallonka ba zan yi ba, saboda abin da nake samu a can ba zan samu ba.

An rufe kasuwannin dabbobi a Jihar Katsina saboda matsalar tsaro, yaya ciniki yake a lokacin da yanzu da aka bude su?

To tsakani da Allah a wancan lokaci an samu matsi sosai, ga karancin dabbobin ga tsada. Wani lokaci babu kayan don masu yankawa a gida ma babu su, ka ga dole ciniki ya ja baya.

Yanzu ga dabbobin amma tsada kusan kullum karuwa take yi, ba ganda kadai ba, yanzu komai kara tsada yake yi, yanayi ne sai addu’a.

Hatta masu gyara mana kai da kafafun sun kara mana kudi, sun ce itace ko gawayin da suke amfani da shi don babbakar tsadar ta yi yawa, wanda suke saya Naira 100 a baya yanzu shi ne Naira 500.

Su kuma mutane in ka yanka masu naman sai su yi maka korafi duk da sanin halin da ake ciki. Akwai wadanda kake koya wa wannan harkar? Sosai. Ka ga dai tare muke yi da yayan nawa kamar yadda na gaya maka, sannan akwai kannena da wadansu yaran.

Kana ganin akwai matsala ga matasanmu game da batun dogaro da kai?

Lallai matasan yanzu suna fuskantar matsala musamman a kan abin da ya shafi dogaro da kai ta fuskar sana’a ko kasuwanci.

Saika ga mutum yana takamar ya yi karatun zamani lallai sai ya samu aiki. Ya duba masu karatu irinsa nawa ke akwai? Na gabansa da na bayansa ko na kasansa nawa ke akwai? Sannan shi aikin musamman na gwamnati da kowa ya yi wa zuru nawa ne?

Saboda haka ina ganin ya kamata matashi ya zage dantse kada ya jira sai an yi masa ko ya yi zaman jiran gawon shanu. Akwai sana’o’in gado da kasuwanci akwai na zamani kowa ya samu ya yi.

Amma matashi ya koma gefe guda ya ce, kamarsa za a ce ya yi sana’ar yin faci a bakin titi, ko ya yi talla ko a ga rigarsa ta yi baki da mai bayan yana da digiri? Ya duba daga lokacin da ya gama karatun nawa digirin ya kawo masa? Ya dubi mai yin facin ko mai tallar burodi nawa yake samu a rana?

To ko kana da wani sako?

Eh, gwamnati da masu hali, yana da kyau duk inda suka ga mai yin sana’a ko kasuwanci musamman matasa, su tallafa masu don kara masu kwarin gwiwa ko ta shawara ko horar da su dabarun sana’ar ko kasuwancin.

Yin haka zai kawo saukin ayyukan assha da wadansu matasa ke yi. Su kuma matasa su yi wa kansu fada su nemi abin yi

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos