Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace?
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan karin wa’adi ya dace ko bai dace ba? Wakilanmu sun tattaro mabambantan ra’ayoyin mutane, kamar haka:
Dokar ba ta dace ba a Adamawa
– Umar Abubakar Sadik
Umar Abubakar Sadik: “Gaskiya karin wa’adin dokar ta baci a Jihar Adamawa bai kamataba amma ta jihohin Borno da Yobe ta yi daidai. Idan ka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa kafin da bayan kafa dokar ta baci a jihohin Borno da Adamawa, an fi samun tashin hankali a wadannan wuraren har wa’adin dokar ta kare a watanni shida da suka gabata. Don haka, ya kamata a gaggauta janye dokar a Jihar Adamawa, sannan su ma jihohin da suka rage, ya kamata a yi nazarin al’amarin da idon basira. Idan aka samu saukin al’amarin, a janye dokar baki daya.”