Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 1

A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]

Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 1
Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 1

A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan karin wa’adi ya dace ko bai dace ba? Wakilanmu sun tattaro mabambantan ra’ayoyin mutane, kamar haka:

 

karin bai kamata ba – Malam Sani

Malam Sani danjarida: “A nawa ra’ayi dai, karin wa’adin dokar-ta-baci a wasu jihohin Arewacin kasar nan da Shugaba Jonathan ya yi bai kamata ba, don hakan ba shi ne zai magance matsalar tsaro a jihohin ba. Idan ka lura, har yanzu an gagara kawo karshen rigingimun. Maimakon haka sai dai ka ji kullum ana ci gaba da kashe mutane, musamman wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba. Saboda haka abin da ya dace gwamnatocin tarayya da na jihohi su yi, kawai shi ne sulhu da su ’yan Boko Haram. A daina sa batun siyasa a cikin lamarin, a yi sulhu na gaskiya tsakanin gwamnati da ’yan ta’adda don a samu zaman lafiya a kasar nan baki daya; don samun walwala da ci gaba mai dorewa.”

 

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54