Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 2

A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]

Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 2
Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 2

A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan karin wa’adi ya dace ko bai dace ba? Wakilanmu sun tattaro mabambantan ra’ayoyin mutane, kamar haka:

 

kara wa’adin dokar ya dace – Fabour Godwin

Fabour Godwin: “Abin da zan iya cewa game da karin wa’adin dokar-ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da Yobe, abu ne da ya dace. Dalilina kuwa shi ne, har yanzu da rina a kaba dangane da al’amarin tsaron yankin saboda ana ci gaba da kai wa jama’ar yankin hare-haren da suke tabka hasarar rayuka da na dukiyoyi. Irin wannan hasarar koma baya ne ga fannin tattalin arzikin yankin da jihohin da ma kasar baki daya. Sai dai abin da ba na goyon baya game da wannan al’amarin yadda kafofin yada labarai suka yi ta shaida wa duniya a watanni shida da suka gabata shi ne, yadda jami’an tsaro suka yi ta shafa wa fuska toka suna cin mutuncin jama’a. Ya kamata duk wanda ke da alhakin tabbatar da tsaro a yankin su sa ido domin gudanar da ayyukansu yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya