Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 3
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan karin wa’adi ya dace ko bai dace ba? Wakilanmu sun tattaro mabambantan ra’ayoyin mutane, kamar haka:
Bai kamata a sa karfi ba – Stanley Buba
Stanley Buba: “Ka ga abin da nake gaya wa jama’a kullum shi ne, a ganina bai kamata a ci gaba da yin amfani da karfi wajen magance batun ta’addanci da wasu rigingimu da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu ba. Talakawa mata da yara suna mutuwa kuma wadannan ’yan Boko Haram sun ki hakura, jami’an tsaro ma sun ki hakura. Ka ga idan aka ci gaba da haka, ina tabbatar maka cewa nan ba da jimawa ba sai a waye gari a tarar ba kowa a wadannan jihohi. Abin da ya dace shi ne, a maida hankali wajen sasantawa tsakanin gwamnati da su ’yan Boko Haram maimakon kara wa’adin dokar-ta-bacin, wanda haka ba zai haifar da da mai ido ba.”