Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 4
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan karin wa’adi ya dace ko bai dace ba? Wakilanmu sun tattaro mabambantan ra’ayoyin mutane, kamar haka:
karin wa’adin takurawa ne
– Musa Yakubu
Alhaji Musa Yakubu Yagarmawa: “Magana ta gaskiya bai dace ba kara sanya wa jihohin Adamawa da Borno da Yobe da Gwamnatin Tarayya ta yi, domin an takura al’ummomin jihohin. Harkar sadarwa babu, kasuwanci ya tsaya kuma ilimi ma ya cutu. Wadda aka sanya a baya ma, kwalliya ma ba ta biya kudin sabulunta ba ballantana a ce an kara wata yanzu.”