Ko kara wa’adin dokar ta baci a jihohi uku ya dace? 5
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]
A makon da ya gabata ne wa’adin da aka sanya wa jihohin Borno da Yobe da Adamawa na dokar-ta-baci ya cika. Nan take Shugaban kasa ya aika wa majalisa bukatar kara wani wa’adin na watanni shida, inda ba tare da bata lokaci ba aka amince masa da karin. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan karin wa’adi ya dace ko bai dace ba? Wakilanmu sun tattaro mabambantan ra’ayoyin mutane, kamar haka:
karin bai dace ba – Muhammad Sani kaura
Alhaji Muhammad Sani kaura: “Gaskiya karin kafa dokar-ta-bacin nan da aka yi wa wadannan jihohi bai dace ba. Dalilina kuwa shi ne, kafin a kafa dokar nan, me ake yi a Adamawa? Zaune suke lafiya fa, ba a yin ta’addancin komai kuma yanzu da aka kafa dokar nan me ake yi a Adamawa? Su kuma sauran jihohin Barno da Yobe, idan ka cire Kano babu inda ake kasuwanci kamar wadannan wurare. Ana haka ne domin a kassara harkar kasuwanci a yankunan.”