Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya?

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban: Zai magance matsalolin Najeriya – Sunusi Muhammad Sunusi […]

Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya?
Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya?

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban:

Zai magance matsalolin Najeriya – Sunusi Muhammad

Sunusi Muhammad: “Ra’ayin shi ne, karin kirkiro sabbin jihohi zai magance matsalar kasar nan, don idan aka sami karin jihohi to za a samu aikin yi a kasar nan. Rashin aikin yi shi ne ya kawo mafiya yawan matsalolin da muke fama da su, kamar matsalar tsaro da matsalar cin hanci da rashawa da dai sauransu. Idan matasa suna samun aikin yi, ba za a samu yawan ta’addanci ba, kamar kashe-kashe da sace-sace da sauransu. Kowace jiha da aka kirkiro, dole a samar da aikin yi, kamar na jami’an tsaro da ma’aikatan jihohi. Amma duk da haka sai idan za a rika ba su isassun kudadensu kamar yadda ake ba tsofaffin jihohi.