Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 1

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban: karin bai da amfani -Alhaji Sani Alhaji  Sani […]

Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 1
Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 1

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban:

karin bai da amfani -Alhaji Sani

Alhaji  Sani Kabir: “Ni a gani na kuma a nawa ra’ayin, karin jihohi ba shi ne abin da kasar nan ke bukata ba; domin ko an kara jihohi ko ba a kara  ba, ba abin da zai  rage cikin matsalolinmu; kila ma sai dai ya kara matsaloli. Abin da Najeriya ke bukata kawai shi ne shugabanni nakwarai amma ba karin jihohi ba. A yanzun nan ba abin da ya samu jihohin da muke da su kuma wasu jihohin da ake da su har yanzu ba su samu ci gaban da ya kamata a ce sun samu ba, idan aka kwatanta su da lokacin da aka ba su jiha. Don haka idan muka samu shugabanni nagari, matsalarmu ta kau.”