Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 2
Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban: karin ba shi ne matsalar Najeriya ba – […]
Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban:
karin ba shi ne matsalar Najeriya ba – Alhaji Garba
Alhaji Garba Cedi: “Abin da Najeriya ke bukata, shugabanni nagari, ba jihohi ba kuma ba yadda karin jihohi zai rage matsalolin da ke addabar kasan nan. Rashin shugabannin kwarai shi ne babbar matsalarmu, muddin dai muka samu shugabannin kwarai to ina tabbatar maka matsalolin mu za su ragu koma su kau. Wasu jihohin ma yau ba a san ko suna nan ba ko ba su nan, domin ko ba su yi kama da jihohi ba. Matsalarmu ita ce, mu samu shugabanni nakwarai. Ni dama za a rage wadanda muke da su ban ga laifi ba, babbar bukatarmu ita ce shugabannin kwarai.