Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 3

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban: Adalci ne zai magance matsalolin Najeriya – Kabiru […]

Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 3
Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 3

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban:

Adalci ne zai magance matsalolin Najeriya – Kabiru Usaini

Alhaji Kabiru Usaini: “kudurin karin jihohi 18 a kasar nan da taron kasa ya kawo ba zai magance matsalolin da ake fuskanta a kasar nan ba. Matsalolin da ake fuskanta a kasar nan ba na karin jihohi ba ne. Babbar matsalar da muke fuskanta a kasar nan ita ce rashin tsaro. Wannan rashin tsaro shi ne ya hana mana zaman lafiya a kasar nan. Kuma an shirya wannan taro kasa ne don gano matsalolin da suke damun kasar nan, tare da bayar da shawarwarin da za su magance wadannan matsaloli. Adalci ne kawai zai magance matsalolin kasar nan ba karin jihohi ba. Domin a yanzu rashin adalci ya lalata komai a kasar nan.