Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 4

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban: Zai kara matsaloli ne kawai – Salisu Maikananzir […]

Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 4
Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 4

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban:

Zai kara matsaloli ne kawai – Salisu Maikananzir

Alhaji Salisu Adamu Maikananzir: ‘’A gaskiya wadannan jihohi 18 da taron kasa ya fitar da kudurin a kara a Najeriya akwai rashin adalci da kabilanci a ciki. Kuma kara jihohi a Najeriya ba zai magance matsalolin da ake fuskanta ba. Don haka karin wadannan jihohi ba shi da wani amfani. Kuma kara jihohi a Najeriya zai kara kawo wasu matsalolin ne, domin a yanzu akwai wasu jihohin ma ba sa iya yin komai.”