Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 5

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban: Ba zai magance matsaloli ba – Nura Musa […]

Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 5
Ko karin jihohi zai iya magance matsalolin Najeriya? 5

Zauren tattauna makomar kasa ya amince da shawarar a kara kirkiro sabbin jihohi 18 a Najeriya. Abin tambaya a wannan muhawara shi ne, shin ko kirkiro sabbin jihohin zai iya magance dinbin matsalolin kasar nan kuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga ra’ayoyin mutane daban-daban:

Ba zai magance matsaloli ba – Nura Musa

Malam Nura Musa: “Ra’ayina shi ne, karin jihohin ba zai magance matsalolin ba sai dai ya kara su, domin a halin da muke ciki a yanzu matsalarmu ba karin jihohi ba, matsalar ita ce cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro a kasa. Idan za a daina cin hanci da rashawa, kuma a sami zaman lafiya to komai ya yi daidai, amma idan an samu karin jihohi kamar yawan kananan hukumomin da muke da su a kasar nan, to ba za a samu saukin matsala ba; sai dai karin matsala.  Sai dai kuma idan neman karin jihohin za a yi shi ne da wata manufa saboda an ce za a raba arzikin kasa, idan aka kara wasu to daman Kudu za su fi yawa don haka za a kashe Arewacin kasar. Wannan a takaice shi ne ra’ayina.”