… Ko Keshi zai samu alawus din Naira miliyan 10?
Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayyana cewa Stephen Keshi zai samu kason Naira miliyan 10 a matsayin alawus dinsa idan ya samu nasarar hayewa da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles gasar cin kofin Afirka na badi amma sai ga shi hakan bai yiwu ba. Hukumar ta kulla yarjejeniya da kocin ne […]
Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayyana cewa Stephen Keshi zai samu kason Naira miliyan 10 a matsayin alawus dinsa idan ya samu nasarar hayewa da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles gasar cin kofin Afirka na badi amma sai ga shi hakan bai yiwu ba.
Hukumar ta kulla yarjejeniya da kocin ne tun kafin kungiyar ta yi wasanni biyu da suka rage watau wasan Kongo da kuma na Afirka ta Kudu.
Shi dai Keshi wanda aka sallama a da, amma daga baya shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayar da umarnin a dawo da shi, kwantaraginsa ta kare da Hukumar ne amma aka dauke shi aiki a matsayin na wucin-gadi. Don haka wannan kudi da za a ba shi ya yi daidai da albashinsa na wata biyu a lokacin da yake matsayin mai cikakken mai horarwa a kungiyar.
Ministan wasanni Mista Tammy Danagogo ne ya tabbatar da wannan labari na biyan Keshi Naira miliyan 10 a wasannin biyu da suka rage wa Najeriya a makon jiya.
Sai dai wannan labari ya karyata batun da Keshi ya yi na cewa ya dawo kungiyar ce don ya cigaba da horar da ita a matsayin kishi ba don kudi ba.