Ko kun san amfanin kofar da ke tsakanin kyamara da fitilar iPhone?

Galibi mutane sun dauka ado ake da su, amma suna da amfani.

Ko kun san amfanin kofar da ke tsakanin kyamara da fitilar iPhone?

Akwai wasu abubuwa da mutane ke amfani da su na yau da kullum masu muhimmanci, amma da yawa ba a san amfaninsu ba. 

Mutane da yawa ba su san cewa wadannan abubuwa na da muhimmanci ba, wasu ma a tsammaninsu abubuwan na ado ne kawai.

Rashin irin wadannan abubuwan zai iya haifar da matsala gare su, ko kuma a masu amfani da su su kasa samun biyan bukata a yayin amfani da su.

Ga wasu daga cikin irin wadannan abubuwan:

’Yar kofar da ke jikin gilas din tagar jirgi

Ta wannan karamar kofa, iska kan shiga cikin jirgi, musamman idan ya keta hazo, tana taimakawa wajen saita iskar da ya kamata ta shiga cikin jirgin.

’Yar kofar da ke tsakanin kyamara da fitilar wayar iPhone

Wannan kofa ba ta ado ba ce, maganadisu ne da ke daukar sauti lokacin kira ko kuma yayin daukar magana ko kuma lokacin daukar bidiyo.

Bakin gilashin fuskar injin makirwe

Wannan kalar gilashin ke tare sinadarin da ke zafafa tare da sanya injin gashin daukar zafi yayin da aka kunna shi, yana kuma taimakwa wajen samar da sinadarin da ke zafafa cikin injin.

Zanen da ke jikin kwararon taya

Zane-zanen da ke jikin kwararo da kwazazzaban da aka yi wa taya sune suke sa abin hawa ya tsaya a yayin da yake gudu bayan an taka burki, sannan suna nuna yanayin dadewar taya da lalacewarta a jikin abin hawan.