Ko kun san watan canjin alkibla?
Mun samu wannan nazari mai muhimmanci a wannan lokaci daga Dokta Uba Ahmad Ibrahim, [email protected] mai lambar waya 07061587787. Ga gundarin nazarin nasa:A duk lokacin da watan Sha’ban ya kama, Musulmi kan fara dokin karatowar watan Ramadan saboda alfarmar da ke cikinsa. To, amma fa shi ma Sha’aban cike yake da falala da ma kuma […]
Mun samu wannan nazari mai muhimmanci a wannan lokaci daga Dokta Uba Ahmad Ibrahim, [email protected] mai lambar waya 07061587787. Ga gundarin nazarin nasa:
A duk lokacin da watan Sha’ban ya kama, Musulmi kan fara dokin karatowar watan Ramadan saboda alfarmar da ke cikinsa. To, amma fa shi ma Sha’aban cike yake da falala da ma kuma wasu lamaura na tarihi da suka faru a cikinsa, a zamanin Manzon Allah (S.A.W).
A Cikin watan Sha’aban din ne Allah Ta’ala Ya biya wa ManzonSa (S.A.W) bukatarsa ta ganin an canja masa alkiblar da yake fuskanta lokacin Sallah, bayan shafe kusan watanni 18 cur da ya yi yana begen ganin hakan ya faru, daga lokacin da ya yi hijira daga Makka zuwa Madina.
Tun daga lokacin da aka ba shi annabta har zuwa wannan lokacin, idan Manzon Allah (S.A.W) zai yi Sallah, alkiblar da yake fuskanta ita ce Masjidul Aksa, wato Masallacin Baitul Makdis da ke garin kudus a Falasdinu.
A lokacin komawa Madina, ganin inda yake fuskanta a zaman alkiblar ya sa Yahudawan Madina suka dinga alfahari, suna cewa fuskantar alkiblarsu da Manzon Allah (S.A.W) yake yi na nuni ne da cewar kwaikwayar addininsu yake yi, don haka su ne gaba da shi, har ma wasunsu na cewa da kamata ya yi ya watsar da Musluncin nasa ya dawo ya bi su cikin addininsu na Yahudanci. Wannan abu ba karamin sosa wa Musulmi [Al-muhajiruna da Ansar] ya dinga yi ba.
Da Allah Ta’ala Ya amsa wa ManzonSa (S.A.W) bukatarsa, Ya sauya masa alkiblar ya komo fuskantar Ka’bah a garin Makka, sai Yahudawan da suka ga an kashe bakinsu, suka fara korafi tare da kokarin dasa shakku da kokwanto a zukatan Musulmi. Suna cewa Manzon Allah (S.A.W) ya yi baki biyu, har ma suka dinga cewa idan alkiblar farko da Manzon Allah (S.A.W) ya dinga fuskanta ita ce ta gaskiya, to yanzu fa Manzon Allah (S.A.W) ya bata ke nan; shi da mabiyansa, in kuma ta yanzu wato Ka’bah ce, to a baya ke nan bautar da ya yi, shi da sahabbansa wahalar banza suka dinga yi.
Wannan abu ba karamin damun sahabbai ya dinga yi ba har sai da Allah Ta’ala Ya saukar da aya tukunna, cikin Alkur’ani, Ya tabbatar da cewa alkiblolin duk nasa ne, duk inda suka fuskanta, kowanne a lokacinsa, ba matsala ba ne, inda Allah din Yake cewa: ‘(Wa lillahil mashriku wal magribu]’ a cikin Suratul Bakara tukunna kafin hankalinsu ya kwanta.
Daga cikin muhimman ayyukan da Manzon Allah (S.A.W) ya saba yi a watan Sha’aban har da yawaita yin azumi na nafila. Hasali ma, Manzon Allah (S.A.W) ba a ga watan da ya fi yawaita yin azumin tadawwu’i a cikinsa fiye da watan Sha’aban ba. Iyalansa, Allah Ya yarda da su, suna fadin cewa Manzon Allah (S.A.W) in ya kama yin azumi a cikin watan har sai sun zaci ba zai daina ba sai ya dire.
Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W) ya fi yawaita azumi a wannan wata fiye da watan Rajab. Kuma in ban da Ramadan lokacin azumin farilla, ba wani wata da Manzon Allah (S.A.W) ya taba azumtarsa baki daya.
Daga nan za mu fahimci cewar masu azumtar watan azumin tsofaffi, duk da cewar muna fatan Allah Ya kara musu kaunar ibada, to amma koyi da Manzon Allah (S.A.W) dai shi ya fi alheri. Manzon Allah (S.A.W) shi da kansa ya fadi cewar a duk wani azumin nafila da Musulmi zai yi, to, irin azumin Annabi Dauda (A.S.) shi ya fi alheri. Yadda Annabi Dauda (A.S.) ke nasa azumin kuma shi ne, idan yau ya yi azumin, to gobe sai ya sha ruwa, jibi in ya yi, gata ya sha ruwa. Irin azumin nafilar da Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W) ya bayyana ke nan da cewa shi ya fi alheri fiye da kowanne.
Ban ce masu azumtar watan Rajab baki dayansa ba su da lada ba, suna da ita, Allah Ya biya su gwargwadon kyawawan niyyoyinsu, amma a addinance, koyi da hakikanin aikin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi, shi ne mafi cancanta a tsaya a kai.
Allah Ya sa mu dace duniya da lahira, Allahumma amin!
***
Rahusa da garabasa a Ramadan
Shi kuma Buhari Daure 07035986444, ya yi mana tambihi ne dangane da rahusa da garabasar da ke kunshe cikin wannan wata mai albarka na Ramadan. Ga abin da yake cewa:
Lokacin watan Ramadan ya kasance lokacin da aka fi kashe kudi wajen ciyar da kai! Duk da cewa ba a cin abinci da rana, amma akan ci da shan abubuwan da ba a ci ko sha a sauran watannin! Kamar naman kaji, kayan ciki, ’ya’yan itatuwa, ganye da dabino.
Kusan kowa ya fahinci a lokacin da ake fara azumi kayan masarufi sun fi tsada a kan kowane lokaci, hakan ya zama wani abu da manazarta ya kamata su mayar da hankali don a kawo sauki.
Duk da cewa wasu su ba su shan jan miya, su kansu kayan miyar sun tashi sama! Amma mene ne hikimar idan ka sayar da tsada, kai ma za ka sayi wani abin da tsada, me zai hana kowa ya hakura da kadan, sauki zai zo ga kowa?
Taimakon talakawa na kawo sauki, tsaro da zaman lafiya! Amma a halin yanzu ba abin da ya rage wa talaka sai a dage da addu’a da karanta Alkur’ani a wannan watan mai alfarma da albarka don samun mafita mai ma’ana.
A wasu kasashe kamar Masar sai da jam’iyyar ’yan uwa suka tabbatar da raguna sun yi araha ta yadda kowa ya yi layya, haka a kasashen Yamma da Amurka idan Kirsmati ta gabato, shagunan rage kudin sayen kaya suke. Me zai hana mu ma jam’iyya mai mulki ta yi irin wannan yunkurin? Kai ko a makwafciyarmu Nijar, sai da gwamnati ta fito da tsarin ba da abinci kyauta da sayarwa da araha don rage radadin talauci.
Don wani ya ce a saukaka, hakan ba zai kawo sauki ba, kai koda mutum ya saukaka sai dai ya sami ladar amma idan al’umma ta saukaka tabbas sauki zai zo! Wasu za su sara, su sayar da riba, bugu da kari mafi yawancin ’yan Najeriya na neman garabasa. Sai mu nema a wajen Ubangiji a watan Rahama.
Idan da gaske ake, me zai hana manyan ’yan kasuwa su sayar da araha, kuma su bude shagunan a ungwanni inda za a sayar da sauki, ta yadda za a sayar daidaiku ga mabukata a farashi mai rahusa. Ko a sara da araha za a sayar da sauki! Tabbas a haka ma madugu zai sami ribarsa. Duk wahalar a kan talaka take karewa, a haka dama ta samu ga masu karamin karfi, su dage da nafilfili da kiyamul-laili, musamman an yi dace azimin ya zo a lokacin damina!
Allah ya kawo mana mafita, Allah sarkin sauki!