Ko kwalliya za ta biya kudin sabulu a sayar da Hukumar samar da wutar lantarki?
“Ba ma tsammanin fannin ya farfado a dare daya, amma muna fatan samun ingancin abubuwa a wani lokaci nan gaba kadan, kamar yadda muka gani a bangaren sadarwa da Bankuna.” Wasu daga cikin kalaman shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan kenan, a lokacin da yake bikin mika ragamar tafiyar da Hukumar samar da wutar Lantarki ta […]
“Ba ma tsammanin fannin ya farfado a dare daya, amma muna fatan samun ingancin abubuwa a wani lokaci nan gaba kadan, kamar yadda muka gani a bangaren sadarwa da Bankuna.”
Wasu daga cikin kalaman shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan kenan, a lokacin da yake bikin mika ragamar tafiyar da Hukumar samar da wutar Lantarki ta kasa wato PHCN, ga wakilan Kamfanoni 15 da suka yi nasarar sayen Hukumarta PHCN, a shirin gwamnatin tarayya na sayar da Hukumar ga `yan kasuwa, bikin da aka yi a ranar 30 ga watan Satumbar da ya gabata a Abuja fadar gwamnatin tarayya.
Yau shekaru takwas ke nan, wato a shekarar 2005, gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ta samar da dokar da ta rarraba Hukumar samar da wutar Lantarkin ta PHCN, a zaman Kamfanoni daban-daban, har guda 18, da aniyar ta sayar da su ga `yan kasuwa walau na cikin gida ko na waje. kididdiga ta tabbatar, a cikin shekaru sama da 14, da ake mulkin dimokuradiyya gwamnatin tarayya ta kashe miliyan zambar dubu 3.2tiriliyon, amma wutar lantarkin ta zama tamfar ciwon ajali gwamma jiya da yau, karfin wutar lantarkin ya tabarbare daga kilowat 4,000, sai da ya fado zuwa 2,000, da yar doriya.
Kamar yadda tsarin ya kasance zuwa yanzu an kasa Hukumar wutar Lantarkin gida uku, akwai Kamfanoni shida wadanda daga garesu ake samun wutar lantarkin kasar nan, irin su Shiroro da Kayinji da Afam da Sapele. Akwai kuma Kamfanoni 11,wadanda su aka dora wa alhakin rarraba wuta a cikin kasa,wato kai tsaye ga dukkan mai bukata (wato su ne masu rarrabawa). An kuma ware wani babban Kamfani da shi ne kadai zai ci gaba da kasancewa karkashin kulawar gwamnatin tarayya, aka kuma mika kwantiragin tafiyar da wannan Kamfani ga Kamfanin Monitoba na kasar Kanada, wanda shi ne kamfanin da zai rika karbar wutar lantarkin daga wadancan Kamfanoni shida, da suke samar da ita, sannan ya mikata ga wadancan Kamfanoni 11 da su za su rabata ga mutanen kasa, ma`ana dai shi ke tsakiya, kuma wakilin gwamnatin tarayya a cikin shirin baki daya.
In ban da wancan Kamfani na Monitoba, sauran Kamfanonin 17, dukkansu, wasu gwamnatocin jihohi da wasu manya-manyan `yan kasuwar kasar nan, musamman masu hada-hadar man fetur da iskar gas da harkokin sadarwa da hadin gwiwar Kamfanonin wasu kwararru akan harkokin wutar lantarki daga kasashen waje su suka saye su.
A cikin gwamnatocin jihohi akwar irinsu Jihar Neja da Bayelsa da Ribas da Kuros Ribas da Akwa Ibom. A jerin `yan kasuwa akwai mutane irinsu Mista Femi Otedola da Alhaji Aminu dantata da Kanar Sani Bello (mai ritaya) da Mista Tonye Cole da Alhaji Hamisu Abubakar, wanda aka fi sa ni da Mai rago da tsohon shugaban kasa JanarAbdussalami Abubakar da Mista Tope Sonubi da Alhaji Mohammed Noma da Sir Emeka Offor da Alhaji Umaru Mutallab da dai sauransu.
A karkashin yarjejeniyar sayar da Hukumar wutar lantarkin, ana sa ran Kamfanoni za su ci gajiyar samar da iskar gas daga gwamnatin tarayya ta riga ta sanya hannu da kamfanin gas na kasa da za ta rika tabbatar da samar da wadatacciyar iskar gas wanda shi ne babban makamashi ga tashoshin da suke samar da wutar lantarkin. Kuma gwamnatin tarayyar ta bayar da tabbaci garesu na kula da ma`aikatar gas din ta fannoni daban-daban. Gas din da babu dalilin da zai sanya a ce ana fama da matsalarsa a kasar nan a matsayin kasar nan ta 9 a cikin kasashen duniya masu arzikin iskar gas.
Bisa ga irin yadda Allah Ya albarkaci kasar nan da arziki da yawan al`umma wanda take na daya a nahiyar Afirka, babu dalilin da zai sanya a ce haske wutar lantarki ya gagari `yankasa, amma sai ga shi yanzu ana kididdigar cewa mutum daya cikin mutum 10 na kasar nan ke samun hasken wutar lntarki, wannan ma molon ka ne. Kar ya yi batun dimbin kudin da aka cusa a kan batun inganta karfin wutar lantarkin. Alal misali rahoton `yan Majalisar Wakilai na shekarun 2008 zuwa 2009, ya tabbatar da cewa an kashe Dala miliyan 15, don inganta wutar, amma dai har yau gwamma jiya da yau.
Rashin wutar nan, ka iya cewa shi ne kusan kashi 50 cikin 100, na matsalolin yau da kullum da na tattalin arziki da kasar nan da al`ummarta suke fama da su, don kuwa a yau kana gyara tsarinsamar da wutar lantarkin, to, kuwa kana shawo kan matsaloli irin na rashin ayyukan yi koda bana manya da kananan masana`antu ba, a`a na cikin al`umma masu son su yi amfani dawutar a cikin gidajensu da wuraren ayyukansu da na sana`o`insu, kar ka yi batun manya da kananan masana`antun da irin dimbin ayyukan da za su samar. Haka labarin yake akan batun noma da kiwo da sauran harkokin yau da kullum.
Rashin karfin wutar lantarkin nan shi ya kara mayar da mu baya a fannoni daban-daban, ta yadda kasashe irinsu Brazil da kuma fara tare yanzu suka yi mana fintinkau ta kowane fanni, ta yadda yanzu Brazil, ba wai kera mota da sauran na`urori ba da ta kware akai, har jirgin kasa da taragonsa take kerawa.
Ina fata wannan cefanarwa da aka yi wa Hukumar wutar lantarki za ta zama gobarar titi ga mutanen kasar nan, ta yadda nan da wani lokaci kasar nan za ta kai gacin da ya kamata ta kai. Kafin lokacin Allah Ya sa gwamnatin tarayya ta rika zuba idanu akan wadannan Kamfanoni da ta sayar wa Hukumar, kar kuma ya zama an bar `yan kasa a hannun `ya jari hujja, ta yadda sai yadda suka yi da sunan suna son su mayar da kudinsu a cikin dare daya