Ko maganganun Obasanjo za su yi tasiri a wannan karo?
Duk ma’abucin bibiyar wannan fili zai tabbatar da cewa, na sha yin tsokaci a kan yadda tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Aremu Obasanjo ya zama karan kada miya ko kadangaren bakin tulu a kan harkokin siyasa da ta zamantakewar kasar nan, tun a 1979 da ya mika mulki ga gwamnatin farar hula ta marigayi Shugaban […]
Duk ma’abucin bibiyar wannan fili zai tabbatar da cewa, na sha yin tsokaci a kan yadda tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Aremu Obasanjo ya zama karan kada miya ko kadangaren bakin tulu a kan harkokin siyasa da ta zamantakewar kasar nan, tun a 1979 da ya mika mulki ga gwamnatin farar hula ta marigayi Shugaban Kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a Jamhuriya ta Biyu.
Tun daga wancan lokaci daidai da rana daya Cif Obasanjo, bai taba barin wata gwamnati walau ta farar hula ko ta soja ta sarara ba. Kama daga gwamnatin Alhaji Shehu Shagari (Oktoban 1979 zuwa karshen 1983) zuwa ta Janar Muhammadu Buhari (ta soja 1984 zuwa 1985), har zuwa ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida (1985 zuwa 1993). Bai soki ta rikon kwarya ta Shugaba Cif Enest Shonekan mai watannin da ba su kai hudu cikakku ba (Agusta zuwa Nuwamba 1993). Amma ya soki ta Shugaban Kasa Janar Sani Abacha (1993 zuwa 1998) wadda ta yi maganinsa, kan ta gaji da gaza-ganinsa, inda ta kama shi ta kuma daure shi rai-da-rai, bayan ta same shi da laifin cin amanar kasa na yunkurin kifar da gwamnatin.
Cif Obasanjo na zaman sarka ne Allah Ya karbi ran Shugaban Kasa Janar Abacha, a ranar 8-06-1998, a lokacin Abacha yana ta kokarin cuku-cuku da murda-murdar yadda zai ya gaji kansa, wato ya yi TAZARCE ta kowane hali, amma sai Allah cikin ikonSa Ya karbi abinsa. Samun wannan dama ce Janar Janar Abdussalami Abubakar ya hau kan karagar mulki, ya kuma yi alkawarin kammala kome na mika mulki ga hannun farar hula cikin wata 11, wato ranar 29 ga watan Mayun 1999. Wannan dama ce ta sanya wasu tsofaffin manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, su ka yi kulle-kullensu, suka sa gwamnatin Janar Abdussalami ta yafe wa Cif Obasanjo, ta kuma sako shi daga zaman gidan jarun. Wadancan tsofaffin sojoji su, suka sake shigewa gaba wajen tabbatar da cewa Cif Obasanjo ya tsunduma cikin harkokin siyasa ka’in-da-na’in, kuma ya zama Shugaban Kasa a inuwar jam’iyyarsu ta PDP.
Haka kuwa aka yi Cif Obasanjo ya tsaya wa PDP, takarar Shugabancin Kasa a zaben 1999, ya kuma yi nasara, har karo biyu 1999 zuwa 2003 da 2003 zuwa 2007.
Kafin ya gama mulkinsa a zango na biyu, sai da Cif Obasanjo ya yi fatali da dukan wadanda suka taimaka masa wajen barin gidan sarka da kawo shi kan karagar mulki, ta yadda suna ji suna gani ya rika wasan kura da shugabannin jam’iyyarsu ta PDP, wajen sauke duk wanda ba ya so ya dora wanda yake so. Hatta wadansu gwamnonin jihohi irin na Filato da Bayelsa, sai da Obasanjo ya sa aka tsige su da karfin tsiya, ya kuma kafa dokar ta-baci a jihohinsu, baya ga harkokin tafiyar da mulki da ya rika yi ba bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin kasa ba. Hatta Mataimakinsa Alhaji Atiku Abubakar, wanda yanzu shi ne dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyarsu ta PDP da kyar ya sha a hannun Cif Obasanjo, don kawai ya nuna ya barranta da TAZARCEN Cif Obasanjo da kuma yana son ya gaje shi.
Bisa ga karewar TAZARCENSA Obasanjo, shi daya tilo, a duk cika da batsewar jam’iyyarsu ta PDP, ya dauko marigayi Gwamnan Katsina Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa da na Bayelsa Dokta Goodluck Jonathan, ya nada ’yan takarar Shugaban Kasa da Mataimakinsa a inuwar jam’iyyarsu, alhali bayan Mataimakinsa Alhaji Atiku Abubakar ya nuna kwadayin ya gaje shi. Da yawa daga cikin wadancan tsofaffin manyan hafsoshin sojoji su ma suna so. To shi ma kansa marigayi ’Yar’aduwa bai tsira da jafa’in Cif Obasanjo ba a cikin kasa da shekara biyu da ya yi, amma kuma an ce ’Yar’aduwan ya fara kosawa da irin katsalandar Cif Obasanjo, an ce wai har ya fara shirye-shiryen ya sa a kama Obasanjo, musamman a kan zargin yadda gwamnatinsa ta batar da Dalar Amurka biliyan 16, don samar da wutar lantarki a kasar nan, amma aka wayi gari ba kudin kuma ba wutar, da ma biliyoyin Naira da gwamnatin Cif Obasanjo ta ce ta kashe don ginawa da gyaran hanyoyi.
Rasuwar ’Yar’aduwa ke da wuya Mataimakinsa Goodluck Jonathan, wanda ’yan adawa suka rika suka da ma sharrin wai dan Cif Obasanjo ne, na hawa shi ma Cif Obasanjo ya sa gwamnatinsa gaba da niyyar ganin sai ya kai ta kasa. Don tabbatar da niyyarsa a wani al’amari mai kama da wasan kwaikwayo, sai da Cif Obasanjo ya tara taron shugabannin mazabarsa, kuma a idanun duniya ya dauko katinsa na dan Jam’iyyar PDP, ya kekketa, ya ce kuma shi da jam’iyyar haihata-haihata, ba shi ba ita har abadan abada. Daga nan ya koma sabuwar Jam’iyyar APC a kaikace. Ko shakka babu Cif Obasanjo ya taimaka matuka ga samun nasarar Shugaba Mahammadu Buhari a zaben shekarar 2015, taimakawar da ya yi ba don Allah ba ko don kishin kasa da al’ummarta ba, illa dai sai don yadda zai ci gaba da cin kasuwarsa ta juya duk wanda ke kan karagar mulkin kasar nan. Bayan ya gama lissafinsa ya ga cewa ba makawa Shugaba Jonathan ya gama faduwa a wancan zabe.
Ko shakka babu kasuwar bukatar da Cif Obasanjo ya yi hasashen zai ci a gwamnatin Mahammadu Buhari, ita ta kai shi yin duk abin da ya yi na barin PDP, a cikin muzanta jam’iyyar. Ya kamata tun farko Cif Obasanjo ya san cewa kasuwar ba mai ciyuwa ba ce, bare har ya samu kayan kasuwa da zai kai gida, tunda ya san cewa Buhari ba wanda zai iya juyawa ba ne, illa dai kada ya bari gwamnatinsu ta fadi a ce sun fadi.
A cikin wannan mulki na Shugaba Bahari, Cif Obasanjo ya yi ta rubuta budaddun wasiku ga Shugaban yana sukar lamirin tafiyar da gwamnatinsa, har ta kai ga ma ya fito karara ya ce kada a sake zaben Shugaba Buhari, don kuwa a fadarsa gwamnatin Buhari ta gaza, kamar yadda ya rika yi wa shugabannin da Buharin ya gada. Amma kuma wani abin rainin hankali da rainin wayon masu kada kuri’a na kasar nan, yanzu kuma Cif Obasanjo, bayan ya zafafa ya koma jam’iyyarsa ta PDP, shi ne kuma kan gaba-gaba wajen tallar lallai sai a zabi tsohon Mataimakinsa a Jam’iyyar PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar. Alhaji Atikun da a baya Cif Obasanjo ya ce idan har ya kara goyon bayansa a cikin harkokin siyasa, kada Allah Ya taba yafe masa. Tirkashi! Mai karatu Cif Obasanjo kuma Baban Iyabo ke nan da Allah Ya dade Yana ara wa ranar harkokin siyasar kasar nan, da bai ara wa kowa irinta ba. A nan Nake tambayar “Ko maganganun Obasanjo za su yi tasiri a wannan karo har Jam’iyyar PDP ta ci zaben Shugaban Kasa?” In har ba ta yi nasara ba, to, kuwa Cif Obasanjo da ire-irensa da yardar Allah daga wannan karo sun daina yin kowane irin tasiri a siyasar wannan kasa. Allah Ka rayar da mu mu yi kallon da za mu ba da labari, amin summa amin.