Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 00

A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya […]

Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 00
Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 00

A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya halarci tantancewar, kamar kuma yadda ya ce a ba iyalan mamatan gurabe uku na aikin kai tsaye, wanda ya ji rauni kuwa, a ba shi gurbin aikin shi ma kai tsaye. Abin tambaya a nan shi ne, shin wadannan matakai sun dace ko ba su dace ba? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga al’umma daban-daban:

 

Matakin ya dace – Ali Abdullahi

Ali Abdullahi: “Babu shakka matakin ya dace, sai dai akwai wani hanzari, a duk lokacin da za a dauki ma’aikata a daina sayar da fom mai yawa. Idan mutum 1000 za a dauka to a sayar da iyakacin 1000 zuwa 1500, domin a magance irin abin da ya faru na turmutsitsi a wajen jarrabawar daukar aiki. Abu na biyu, gwamnati ta yi kokarin samar da ingantattar wutar lantarki domin a samar da ayyukan yi ga matasa. Ko ni din nan da a ce da akwai wutar lantarki da zan iya daukar ma’aikata sama da mutum 15, wanda kuma a duk wata zan biya su albashi daga N25,000 zuwa sama, amam saboda rashin wuta a yanzu haka kamfanin a rufe yake. Sannan su kuma matasa su daina dagewa sai aikin gwamnati kawai za su yi.”