Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 01

A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya […]

Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 01
Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 01

A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya halarci tantancewar, kamar kuma yadda ya ce a ba iyalan mamatan gurabe uku na aikin kai tsaye, wanda ya ji rauni kuwa, a ba shi gurbin aikin shi ma kai tsaye. Abin tambaya a nan shi ne, shin wadannan matakai sun dace ko ba su dace ba? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga al’umma daban-daban:

 

Na goyi bayan matakin Jonathan – Umar Garba

Umar Garba: “A ganina, wannan hukunci da Shugaban kasa Jonathan ya yi dangane da badakalar Hukumar-Shige-Da-Fice Ta kasa kan dakatar da yunkurin daukar ma’aikata da ta yi, wadda rububin hakan ya jawo rasa rayukan mutane da dama, hakan ya yi dai-dai. Domin a bisa dubawar da na yi, kasancewar ni ma akwai abokaina biyu da suka rasu sanadiyyar hakan, nake jaddada goyon bayana dari bisa dari kan wannan matsayi na Shugaban kasa na ba da umarnin dakatar da wannan kuduri na hukumar na daukar ma’aikata. Haka nan matakin ba da guraban aiki ga iyalen wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka ji raunuka kai tsaye, a gaskiya shugaban ya yi hakan bisa sanin ya kamata.”