Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 02

A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya […]

Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 02
Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 02

A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya halarci tantancewar, kamar kuma yadda ya ce a ba iyalan mamatan gurabe uku na aikin kai tsaye, wanda ya ji rauni kuwa, a ba shi gurbin aikin shi ma kai tsaye. Abin tambaya a nan shi ne, shin wadannan matakai sun dace ko ba su dace ba? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga al’umma daban-daban:

Matakin ya dace – Malam Aminu

Malam Aminu Muhammad Mararraba: “A gaskiya wannan mataki ya dace, don zai rage taimaka wa wadanda lamarin ya shafa asara. Kodashike ba zai iya biya musu wannan asarar ba. Don ba a sayen rai da kudi ko wata kadara ba. Amma gaskiya Shugaban kasa ya yi kokari kuma ya kamata a rika sa ido a harkokin wadannan hukumomi don kaurace wa aukuwar wannan lamari nan gaba. Don wani lokaci koda mutane 100 ne kawai za su kwasa a aiki za ka ga suna ta sanar da jama’a da dama, daga karshe za ka ga sun kwashe mutane kadan ne kawai. Babban abin da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta rika yi, shi ne ta rika kula sosai.”