Ko matakin da Jonathan ya dauka game da matsalar da ta faru wajen daukar ma’aikatan Hukumar Shige-Da-Fice ta dace? 03
A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya […]
A kwanakin baya ne Hukumar-Shige-Da-Fice ta Najeriya ta gudanar da jarabawar tantance dinbin mutanen da suka bukaci aiki da ita, inda a sanadiyyyar turmutsitsi mutane 20 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji rauni. A sakamakon haka Shugaban kasa ya soke sakamakon tantancewar, ya ce a mayar da kudin fom ga duk wanda ya halarci tantancewar, kamar kuma yadda ya ce a ba iyalan mamatan gurabe uku na aikin kai tsaye, wanda ya ji rauni kuwa, a ba shi gurbin aikin shi ma kai tsaye. Abin tambaya a nan shi ne, shin wadannan matakai sun dace ko ba su dace ba? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga al’umma daban-daban:
Matakin ya yi daidai – Kabiru Salisu
Kabiru Salisu: “A ra’ayina, matakin ya dace kwarai da gaske, domin zai sanyaya ran iyalan wadannan mutane da suka sami kansu a cikin wannan hali. Kiraye-kirayen da jama’a ke yi na a cire Ministan Al’amuran Cikin Gida ba zai magance wannan matsala ba. Abu ne ya riga ya faru. Kowa ya san cewa idan kwanan mutum ya kare ba zai kara ko sakan daya ba. A karshe ina shawartar gwamnati da ta samar wa da matasa aikin yi.”