Ko matakin gwamnati na rancen kudin ‘yan fansho Naira tiriliyan 2 ya dace?
Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda a yanzu Gwamnatin Tarayya ke shirin rancen kudaden ‘yan fansho. Mutane sun bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan shirin. Ga yadda suka bayyana ra’ayoyin nasu: Karbar rancen ba amfani – Aliyu Suleiman Abubakar Daga Muhammad Aminu Ahmad Maiduguri Maganar gaskiya bai kamata a ce za […]
Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda a yanzu Gwamnatin Tarayya ke shirin rancen kudaden ‘yan fansho. Mutane sun bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan shirin. Ga yadda suka bayyana ra’ayoyin nasu:
Karbar rancen ba amfani – Aliyu Suleiman Abubakar
Daga Muhammad Aminu Ahmad Maiduguri
Maganar gaskiya bai kamata a ce za a taba kudin mutanen da suka shafe shekara 35 suna bautawa Gwamnati sun tara kudin da shi ne rayuwarsu, da shi za su taimaki iyalansu da kansu, amma a ce wai Gwamnati zata karbi wannan kudin a matsayin rance, shin idan gwamnati ta dauki kudin rance zuwa yaushe zata biya su, wannan lamari gaskiya ina bawa Gwamnati shawara da kada ta kuskura ta taba kudin ‘yan fansho. Bashin da ake karbowa a manyan kasashe irin su Amurka, Ingila da Faransa an daina ne, menene yasa sai kudin ‘yan fansho za a taba.
Bai dace a karbi rancen ba – Malam Hamza
Daga Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna
Malam Hamza Muhammad, ya ce “Saboda shi Muhammadu Buhari ke cewa, ya dace a rika biyan ‘yan fansho hakkokinsu kuma a yanzu haka ma ce-ce ku-ce ake yi akan yawan ciwo bashi da gwamnatinsa ke yi, kuma a yanzu a ce za a ranci kudin ’yan fansho, ai hakan bai dace ba. Inda ya tabbatar da ba za a ci kudin ba.
Gaskiya bai dace ba – Kwamrade Muktar
Daga Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna
Kwamrade Muktar Muhammad shugaban Mai’aikatan Kwalejin kimiyya da fasaha (Polytechnic) Kaduna ya ce, gaskiya bai dace ba gwamnati ta taba kudin ‘yan fansho domin kasar nan nada dukiyar da ba sai an taba kudin ‘yan fansho ba, za a yi wa kasa aiki. Saboda haka bama goyan bayan matakin gwamnatin.
Bai dace ba – Yusuf Nadabo Zakin Nama
Daga Muhammad Aminu Ahmad Maiduguri
A gaskiya a nawa ra’ayin sam bai dace ba, domin basussukan da aka karbo a da ma menene aka yi da shi, saboda haka, kamata ya yi ita Gwamnati tarayya ta sake tunani akan taba wannan kudi na ‘yan fansho, kuma Shugaban kasa ya tuna cewa yawan cin bashi, ba wani amfani da zai kawo wa kasar nan, da ace wadan can kudaden da aka karbo, an yi wa al’ummar Arewa wani abu da muka gani a kasa, da sai muce dan dama dama, amma ba bu komai kuma ace za a debi kudin ‘yan fansho da sunan rance, ba dai dai bane.
Bai dace ba –Ibrahim Muhammad Yusuf
Daga Lubabatu Garba, Kano
Ni a ra’ayina bai dace gwamnati ta dauki wannan mataki ba. Saboda bashin da ake karbowa ya yi wa kasar yawa, kuma abin takaicin shi ne idan an karbo kudin ba za a yi abin da aka karbo kudin dominsa ba.
Kudin a aljihunsu za su zuba kawai – Kabiru Idris
Daga Lubabatu Garba, Kano
Bai kamata gwamnati ta karbo kudin ba domin ba ‘yan kasa ne za su amfana da kudin ba shugabannin ne za su kwashe kudin su zuba a aljihunsu kawai. Kowa ya san na ‘yan fanshon ne za a ba kudin ba, saboda su ‘yan fansho suna da kudinsu daban da ake tara musu daga albashinsu da kuma wanda ake warewa daga lalitar gwamnati.