Ko matasan Zamfara na da amfani a wajen hukuma?

A Jihar Zamfara an fara aikin gina barikin soja don tabbatar da tsaro, amma abin takaicin shi ne, matasanmu ba a ba su dammar aikin leburanci ba, ta yadda aikin zai fara yin tasiri a kansu. Wannan matsaya da aka dauka don aiwatar da kwangilar a birnin Gusau, za ta sanya mutum ya ribka tunanin […]

Ko matasan Zamfara na da amfani a wajen hukuma?
Ko matasan Zamfara na da amfani a wajen hukuma?

A Jihar Zamfara an fara aikin gina barikin soja don tabbatar da tsaro, amma abin takaicin shi ne, matasanmu ba a ba su dammar aikin leburanci ba, ta yadda aikin zai fara yin tasiri a kansu. Wannan matsaya da aka dauka don aiwatar da kwangilar a birnin Gusau, za ta sanya mutum ya ribka tunanin ko matsa ba su da amfani a wajen hukuma?
Duniya kaf! Ta san halin da dan uwa matashin Najeriya yake fama da shi na rashin ayukkan yi, wanda hakan kan sa da dama daga cikin mu matasa kan yi bkaura daga garuruwanmu da ma bkasarmu kwata, domin neman abinci ido rufe!
Da dama daga cikin al’ummar Jihar Zamfara ne kan bar Zamfara  zuwa kudancin Najeriya, da sunan leburanci da bkananan sana’o’in da za su tallafa wa rayuwarmu. Duk da wulabkanci iri-iri da muke fuskanta bai sa mun ja baya ba. Yanzu haka dubban matasanmu sun  bar bkasarmu Najeriya zuwa Arlit ta bkasar Nijar da sunan ginar zinari duk da kashe wasunmu da aka yi, wasu kuma su kwaso miyagun aljannu, duk hakan bai sa mun ja baya ba. Domin tunanin mu dace.
A nan ya kamata Shugabanninmu su tashi tsaye domin ganin sun tsamo mu daga cikin wannan mawuyacin halin da muke fadawa a wannan balaguron da muke yi, amma sai dai kash! Suna nuna halin ko-in-kula.
Kwatsam!  Sai muka ji an bayar da kwangilar gina barikin sojoji a garin Gusau, wanda wannan ya sa muka cika da murna ganin cewa, da dama daga cikin mu ne za su samu damar neman abinci a wannan katafaren aiki! Amma sai dai Kash! Bayan dauko kamfanin da zai yi kwangilar aikin daga bkasar Malesiya, wanda bai yi mana ciwo bkwarai ba.
Don ina ganin bkila akwai wani tsarin da su suke so a yi musu na aikin, wanda bkila a bkasata Najeriya, babu kamfanin da ke da wannan bkwarewar, amma babban abin da ya fi bai wa talaka mamaki, shi ne da aka ce ba a bubkatar ko da leburorin da za su yi aiki a wannan aiki. Wannan ya nuna shi matashi ba shi da wani amfani a Jihar Zamfara, sai ko in lokacin zabe ya bkarato, a ba mu kayan maye mu taka da su, mu kwana tare da su a kowane daji! Amma yanzu tun da lokacin zabe ya kwanta dama, shi ke nan. Ba wani tunani na kimtsa mu, tare da dawo da mu akan turba tagari.
Don haka muna kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da duk wani mai hannu a wannan kwangilar, musanman ministan tsaro, wanda Alhamdulillahi Bazamfare ne, wato Burgediya-Janar Mansur dan-Alin Birnin Magaji,  da su tabbatar cewa, an dauki lebororin Jihar Zamfara, domin rage mana radadin rashin ayyukkan yi da kuma sama mana ayukkan da za mu samu abinci.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau, shi ne, Jami’in Hulda da Jama’a na bkungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Zamfara) 08069807496 [email protected]