Ko mutuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba za ta sa Gwamna Suntai ya dawo kan kujerarsa?
A ranar Litinin din makon da ya gabata ne Allah cikin ikonSa ya karbi ran Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba Mista Haruna Tsokwa, a Cibiyar kiwon lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo babban birnin jihar, bayan wata ’yar gajeriyar rashin lafiya. Kamar yadda wani dan uwansa ya fadawa manema labarai bayan mutuwarsa, tsohon Kakakin […]
A ranar Litinin din makon da ya gabata ne Allah cikin ikonSa ya karbi ran Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba Mista Haruna Tsokwa, a Cibiyar kiwon lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo babban birnin jihar, bayan wata ’yar gajeriyar rashin lafiya. Kamar yadda wani dan uwansa ya fadawa manema labarai bayan mutuwarsa, tsohon Kakakin Majalisar ya je atisaye a ranar Talatar wancan makon, amma bayan ya dawo gida, sai da aka taimaka masa ya iya shiga gida, halin da ya sanya aka gayyato Likitansa, wanda bayan ya auna shi ya tabbatar da cewa jininsa da yawan sukarinsa, sun yi mugun hawa.
A irin wannan hali ne, aka ci gaba da kula da shi a tsaitsaye kuma ya ci gaba da zuwa ofis. Ko ranar da zai mutu, dan uwan nasa ya tabbatar da cewa tsohon Kakakin ya samu yin addu`a shi da iyalinsa da asuba, har ma ya kimtsa da niyyar zai tafi ofis, sai ya yanke jiki ya fadi, abinda ya sa aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo, inda a can Allah Ya karbi ransa a wannan safiyar. Ya rasu yana dan shekaru 47. Ana sa ran yin bikin bizne shi a ranar 28 ga wannan watan. Marigayi Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ta Taraba da yake wakiltar mazabar Takum ta daya, an zabe shi ne akan wannan mukami ne a ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, bayan `yan Malisar sun tsige Mista Istifanus Gbana da mataimakinsa, bisa zarginsu da gazawa cikin gudanar da ayyukansu.
Marigayi Haruna Tsokwa ya hau kan karagar mulkin Majalisar Dokokin Jihar ta Taraba a daidai lokacin da ake cikin tsakiyar rudanin rashin lafiyar Gwamnan Jihar Mista danbaba danfulani Suntai, tun bayan da ya yi hadari da jirgin samansa da yake tukawa da kansa kusa da filin jirgin saman Yola babban birnin jihar Adamawa a ranar 26 ga watan Oktoban bara, hadarin da ya sanya ala tilas aka garzaya da shi zuwa assibitin kasa dake Abuja, daga can kuma aka wuce da shi wani asibiti da ke kasar Jamus, a can din ma aka sake wucewa da shi kasar Amurka, duk da aniyar neman magani.
Duk wannan dambarwa da ake ciki a jihar, tuni Majalisar Dokokin jihar ta mika ragamar iko ga Alhaji Garba UTC, a matsayin mai rikon mukamin gwamnan jihar, bisa ga tande-tanaden kundin tsarin mukin kasar nan, amma bambance-bambancen addini da kabilanci kai har ma da na jinshi suke ci gaba da fadada. Don haka hawan Alhaji Garba UTC kan mukamin mai rikon gwamnan ke da wuya, da kuma irin yadda aka samu canjin shugabancin tafiyar da Majalisar Dokokin jihar, Majalisar da ta bada umurnin a kori wasu Kwamishinoni biyar da Sakataen gwamnatin jihar da wasu Mashawarta na musamman biyu, wadanda dukkansu aka ce na hannun daman gwamna Suntai ne, bisa ga samunsu da MajalisarDokokin jihar ta yi da laifin yin sama da fadi da kudaden taimakon ambaliyar ruwan saman bara, sama da Naira miliyan 400, mutanen da mukaddashin gwamnan ya amince ya sallame su a ranar 25-07-13, sai harkokin siyasar jihar ta Taraba suka kara rinchabewa
Sallamar wadancan manyan jami`ai da ake kallon na hannun daman Gwamna Suntai ne da kuma a irin lokacin da ta zo, wato a daidai lokacin da ake ta zaman jiran gwamna Suntai zai dawo yau, zai dawo gobe, hakan sun kara iza wutar kiyayyar da ake ciki a jihar, har al`amarin ya kawo darewar Majalisar Dokokin jihar gida biyu, daya bangaren mai Wakilai 16, yana tare da Kakakin Majalisar mai mutuwa, daya kuma mai Wakilai 8, yana karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye. A zamantakewa,irin ta jihar Taraba, jihar da ta kunshi kashi 40, musulmi, kashi 40, Kirista, sauran kashi 20, kuma Arna ne wadanda sau tari suna tare da mabiya addinin Kirista.
Kokowar karbar mulkin jihar, tsakanin Gwamna Suntai da mataimakinsa Alhaji Garba UTC ba ta taso gadan-gadan ba, sai bayan dawowar Gwamna Suntai daga wurin jinya, a ranar 24-08-13. Gwamnan da tun saukarsa a filin jirgin saman Abuja mutane irin su Farfesa Jerry Gana da suka tarbesa suka ce ya warke sarai kuma zai iya komawa bakin aiki, alhali kowa ya gani cewa a rike ake da shi a lokacin da yake saukowa daga jirgin da ya kawo shi, kuma bai iya cewa da kowa uffan ba ciki har da manema labarai a Abujan balle kuma a Jalingo.
Duk da waccan shaidar zur ta su Farfesa Jerry Gana da irin yadda aka gabatarwa da mutanen jihar wani jawabi ta gidan Talabijin din jihar aka ce gwamnan ya yi shi duk sun ci gaba da jefa shakku a zukatan mutane akan anya Gwamna Suntai ya san abin da yake yi?
Kwanaki uku bayan isar gwamna Suntai Jalingo, bisa ga tanadin tsarin mulkin kasar nan, gwamnan ya rubutawa Majalisar Dokokin jihar takarda yana sanar da su ya dawawo kuma zai koma bakin aikinsa, amma sai Kakakin Majalisar marigayi Mista Haruna Tsokwa, ya nemi bayyanar gwamna Suntai gabansu, ta yadda `yan Majalisar za su iya tantance cikakkiyar lafiyarsa, kafin su amince da bukatarsa, al`amarin da ya faskara, kai hatta ma gani da ido, sai da `yan Majalisar suka yi wa uwargidan Gwamnan Madam Hauwa Suntai barazanar za su tsige mijin nata, kana ta bari suka gan shi, ganin da ya tabbatar masu da cewa gwamnan bai warke ba, don haka suka zartas da kudurin ya ci gaba da neman magani har zuwa lokacin da ya samu lafiya.
A bisa wannan hali Kakakin Majalisar marigayi Tsokwa ya fadi ya mutu, abinda ya kawo a ranar Litinin din wannan makon aka zabi Mista Tanko Maikarfi a matsayin sabon Kakakin Majalisar Dokokin jihar, wanda kafin a zabe sa shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye na Majalisar da ya fito daga mazabar Wukari ta daya, wanda kuma kafin zabensa yana cikin wadancan `yan Majalisa 16 da suke tare da marigayi tsohon Kakakin.
Dadin dadawa kuma a cikin jawabinsa na kama aiki sabon Kakakin ya sha alwashin yin aiki cikin kamanta gaskiya da adalci, sannan ya nemi `yan uwansa `yan Majalisa da lallai su hada kai, yana mai nuni da cewa ”Idan har muka haba kai zai yi wuya mu kasa cimma nasara, amma da zarar muka rarrabu ba za mu iya cimma burinmu ba. Da wannan sabon shugabanci a Majalisar Dokokin ta jihar Taraba da irin mutumin da aka zaba, da irin jawabinsa, mai karatu za ka san cewa da wuya kowace irin matsin lamba za a samu Gwamna Suntai ya dawo kan karagar mulkin jihar ba tare da ya samu cikakkkiyar lafiya ba.