Ko na yi aure zan ci gaba da sana’ar wanzanci —Hassana

Hassana Gambo mai sana’ar wanzanci matashiya ce wacce ke ajin karshe na sakandire a Jihar Kano.

Ko na yi aure zan ci gaba da sana’ar wanzanci —Hassana

Sana’ar wanzanci dadaddiyar sana’a ce da ke cikin jerin sana’o’in gargajiya wadanda Bahaushe ya gada kaka da kakanni.

A bisa al’ada maza ne ke gudanar da ita; Sai dai a wannan lokaci Aminiya ta ci karo da wata mace matashiya da ke gudanar da wannan sana’a ta wanzanci.

Hassana Gambo matashiya ce wacce ke ajin karshe na sakandire a Jihar Kano.

Duk da cewar tana karatu hakan bai hana ta gudanar da sana’ar da ta gada ta wanzanci ba.

Hassana wacce ’ya ce ga Alhaji Gambo, Shugaban kungiyar Wanzamai na karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano da ke gudanar da duk wasu ayyuka da masu sana’ar wanzanci ke gudanarwa, kamar aski da kaciya da kaho da cire beli da tsagun gargajiya da sauransu.

Hassana ta shaida wa Aminiya cewa, ta fara gudanar da sana’ar wanzanci tun tana ’yar shekara 10, lokacin da mahaifinta ya fara koya mata

“Duba da cewa ita wanann sana’a ita ta haife mu, domin tun daga kan kakannina suke gudanar da wannan sana’a sai mahaifina ya fara koya min kanana-kanan abubuwa na wannan sana’a kamar yin aski.

“Ya kasance idan zai je yi wa jarirai aski, yakan tafi da ni yana nuna min yadda ake yi.

“Yau da gobe ina koyo ni ma har na iya.

“A yanzu haka nakan iya yin aski na manya ko na yara.”

A cewarta, aikin wanzancin da ya fi ba ta wuya shi ne kaho da kuma kaciya.

“Duk a wannan sana’ar abin da na fi samun wahalar koyon sa shi ne kaho.

“Kin san da yake shi kaho na gargajiya wanda ake yi da kahon shanu ana sa baki a zuko jini, to wannan shi ma yana ba ni tsoro.

“Haka ita ma kaciya lokacin da na fara yi ina tsorata saboda irin jinin da yake fita daga jikin yara, sannan kuma ba na son na ga yaran suna kuka.”

Game da batun cire beli, Hassana ta bayyana cewa akwai fa’ida wajen cire wa yara beli da kuma angurya da ake cire wa mata, duk da cewa a yanzu mutane suna kin hakan.

“A gaskiya cire beli abu ne mai kyau domin idan har ba a cire wa yaro ba, to ko ya girma zai zame masa matsala, domin wani ma ko abinci ba ya barin sa ya ci saboda zai yi ta tofo ya hana shi sakewa.

“Haka ita ma mace idan ba a cire mata angurya ba, to za ta samu matsala a gidan aurenta.

“Duk da dai mutane a yanzu suna nuna kyama ga cire beli da kuma angurya, amma mun san cewa abubuwa ne da suke da amfani sosai.

“A yanzu mu ma muna bayar da maganin da ake sha yana narkewa, sai dai har zuwa yanzu ba a samu maganin da ake sa wa mace a gabanta don ya dauke mata wanann angurya ba.”

Haka kuma a cewar Hassana rashin yin aiki daidai ne yake sanya wa a samu matsala yayin cire beli.

“Kin san ana yin amfani da dogari a danne harshe da shi, sai kuma a dauko koshiya a sa a cire belin.

“Sai dai akwai iya ka’idar da ake cirewa.

“Idan mutum ya zarce shi ne ake samun matsala har jini ya balle.

“Haka kuma ita ma a bangaren mace akwai iyakar wurin da ake cirewa wanda kuma da zarar an zarce iyakar, to fa shi ma za a iya samun matsala.

“A takaice ina nufin ketare iyaka ne ke janyowa a samu matsala a wajen cire beli da angurya.

“Ni kuma tunda nake yi ban taba samun matsala ba”

A cewar Hassana tana alfahari da sanaa’arta wadda za ta iya dogaro da ita a nan gaba.

“Ni ina alfahari da sana’ata ta wanzanci kuma zan ci gaba da yin ta ko a nan gaba.

“Domin na dauki alkawari ko aure na yi zan ci gaba da sana’ata.

“Duk mijin da zai aure ni, zan gaya masa wannan.

“Kuma ko da na samu damar yin karatu mai zurfi a nan gaba, ba zan bar sana’ar wanzanci ba.”

Ba wai kawai ayyukan wanzanci kadai Hassana ke yi ba, hatta a sha’anin wasanni na wanzamai ba a bar ta a baya ba.

“Nakan shiga a fafata da ni a harkokin wasanni namu na wanzamai, irin wasannin da muke gudanarwa na siddabaru kamar wasan cin reza da wasan da mutum ke sa aska ya jujjuya ta a cikin bakinsa.

“Ko kuma a yi wa kwarya kaho jini ya fito. Ko kuma a zuba ruwa a buta a sa tsinke a ciki ya tashi sama.”

Hassana ta musanta zargin da ake yi cewa akwai tsafi a ciki.

“Gaskiya ba mu yin tsafi a al’amuranmu gaba daya sai dai mu yi addu’a kawai.

“Kuma sai ki ga cikin ikon Allah mun yi wasanmu mun gama lafiya”

A cewar Hassana, tun daga lokacin da ta fara wannan sana’a ba ta taba samun wani tallafi ko horo daga gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu ba, duk kuwa da cewa an sha yi musu alkawura da dama.

“Sai dai ta yi kira ga gwamanti da ta taimaka musu da kayan aikin zamani yadda za su bunkasa sana’arsu.

“Mu a nan da kika ganmu ba mu taba samun wani tallafi daga gwamnati ko wasu kungiyoyi masu zamn kansu ba.

“Muna dai kira ga gwamnati da ta taimaka mana ta gyara mana shagon da nake gudanar da sana’ar kasancewar wurin turbaya ce.

“Ina so a taimaka min a zamanantar min da wurin yadda zai ja hankalin masu zuwa.

“Haka kuma ina bukatar kayan aiki na zamani, saboda samun saukin gudanar da ayyuka.

“Kin ga yanzu ba kowa ne ke bukatar a yi masa amfani da askar gargajiya ba.

“Mutane sun fi son askar zamani. Haka kuma kin ga a yanzu ba a fiye amfani da kaho na gargajiy wajen yin kaho ba.

“Akwai wani famfo da ake amfani da shi a zamanance a maimakon yin amfani da kaho.

“Haka kuma ko kujerunmu muna bukatar na zamani duba da cewa a yanzu muna amfani da benci”

Hassana ta bayyana cewa, a yanzu ta fara koya wa kanwarta wannan sana’a domin har ta kai ita ma tana iya yin aski.

“Ni ma a yanzu na fara koya wa kanwata wannan sana’a tamu.

“Idan ya kasance zan je askin jarirai nakan dauke ta mu tafi tare ta yi komai lafiya.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos