Ko nade-naden mukaman da Shugaba Jonathan ke yi sun dace?

A yayin da ya rage kasa da wata daya ya sauka daga mulki, Shugaban kasa Goodluck Jonathan yana ta nade-naden mutane a mukamai daban-daban. Ya nada sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda, ya nada Shugaban Hukumar Jiragen Ruwa da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin wadannan nade-nade ko sun dace? Ga abin da mutane […]

Ko nade-naden mukaman da Shugaba Jonathan ke yi sun dace?
Ko nade-naden mukaman da Shugaba Jonathan ke yi sun dace?

A yayin da ya rage kasa da wata daya ya sauka daga mulki, Shugaban kasa Goodluck Jonathan yana ta nade-naden mutane a mukamai daban-daban. Ya nada sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda, ya nada Shugaban Hukumar Jiragen Ruwa da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin wadannan nade-nade ko sun dace? Ga abin da mutane suka ce:

Nade-naden da Jonathan ke yi neman bata wa Buhari mulki ne -Rabi’u Tela

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

A ra’ayin Rabi’u Tela da ke zaune a bashama Road Tudun Wada Kaduna, “a gaskiya nade-naden da kuma sauke-sauken mukamai da Gwamnatin Shugaba Jonathan mai barin gado yake yi a halin yanzu neman ya bata wa Shugaba Mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari mulki ne. In ba haka ba, ta yaya za a ce shugaban da zai tafi a kasa da wata daya daga yau ya rika yin nade-nade da kuma sauke-sauke babu gaira babu dalili? Don haka akwai dai lauje cikin nadi, kuma ni ban gamsu da abin da Jonathan yake yi na nade-nade a halin yanzu ba”.

Abin da Jonathan ya yi bai dace ba -Nafi’u Hussaini

Nafi’u Hussaini mazaunin Tudun Wada Kaduna ya bayyana ra’ayinsa da cewa bai dace shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya rika yin nade-nade da sauke-sauke a wannan lokaci ba.  Yadda kwanaki kadan suka rage masa, zan iya cewa yana so ne ya cimma wata boyayyar manufa kurum, musamman neman kawo rudani ga gwamnatin da ke tafe.  Don haka ni ban goyi bayan shugaban a kan wannan abu da yake yi ba.

Ba su dace ba – Hudu Umar

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Malam Hudu Umar: “A gaskiya wadannan nade-nade da Shugaba Goodluck Jonathan yake yi a daidai lokacin da zai bar gado ba su dace ba. Wannan fargar jaji yake yi tare da hauka da wayo. Dalilina shi ne, mene ne ya hana shi yin irin wadannan nade-nade tun tuni sai yanzu? Yana so ne ya gadar da wasu matsaloli ga zababben Shugaba Muhammadu Buhari da yake jiran gado, ta yadda matsalolin za su bata masa suna. Ya kamata shugaba mai jiran gado ya yi watsi da irin wadannan nade-nade idan ya kama ragamar mulkin kasa.”

Ba su dace ba ko kadan – Surajo Ibrahim

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Surajo Ibrahim: “Ni dai a tawa fahimtar, bai dace Shugaba Goodluck Jonathan ya rika nada mukamai tare da korar wasu daga kan mukamansu ba. Dalilina shi ne, ni dai na sani cewa ana nada mutane bisa wasu mukamai domin su yi wa kasa aiki, to wane lokaci wadannan sababbin nade-nade za su samu su yi aikin da ake so cikin dan kankanen lokaci da ubangidan nasu zai tattara nasa-ya-nasa ya fice daga gidan gwamnati? Na hango cewa sabuwar gwamnati mai jiran gado ba za ta tafi tare da wadannan sababbin mutane da aka nada bisa mukamai ba saboda haka nadin nasu bai da wani amfani ko kadan. Shugaba Jonathan yana so ne ya bar baya da kura, amma Allah Ya fi shi.”

Nade-naden bata lokaci ne – Nasiru Gwallaga

Hamza Aliyu, a Bauchi

Nasiru Umar Gwallaga: “Abin da Jonathan ya kamata ya fara yi shi ne, ya kwashe dukkan kayayyakinsa daga fadar gwamnati sannan kuma ya mika dukkan kayayyakin gwamnati ga sabon Shugaban kasa nade-naden mukamai da yake ci gaba da yi yana bata wa kansa lokaci ne. Saboda haka ina ba da shawara, al’umma su kwantar da hankalinsu, muna tabbatar wa talakawa cewa duk abubuwan da wannan gwamnati ta yi wanda ya saba wa doka sai mun tona musu asiri ta kafofin watsa labarai.”

Nade-naden ba su da wani amfani – Kawule Gamawa

Hamza Aliyu, a Bauchi

Shehu Kawule Gamawa: “Maganar gaskiya, kowa ya san cewa sabbin mukaman da Shugaba Jonathan ke ci gaba da nadawa ba su da wani amfani a tsarin dimokuradiyyar Najeriya; domin tun lokacin da ya karbi ragamar shugabancin kasar nan a 2011, babu wani sauyi da ’yan kasar suka samu saboda haka ya makara kuma muna fatar sabuwar gwamnati da za ta shigo nan da makonni kadan masu zuwa ta rusa duk wasu mukamai da aka nada, wadanda suka saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999. Kuma sabon shugaban ’yan sanda da aka nada na riko ya kamata a yi garambawul.”