Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata?

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka […]

Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata?
Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata?

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu:

 

A gaskiya ba zai biya bukata ba -Sani Shokin

Muhammad Sani Shokin, Sarkin Samarin Tudun Wada Kaduna:  A gaskiya nadin da za a yi maimakon a bar al’umma su zakulo wakilai da kansu bai dace ba.  Dalili kuwa shi ne duk wanda aka ce an nada ne maimakon zabe to alal hakika idan ya wakilci taron ba shi da ra’yinsa ko na al’umma sai abin da gwamnati ta bukaci ya yi.  Don haka ba na tsammanin za a samu biyan bukata ta hanyar nadi maimakon zabe.  Duk wanda aka nada zai je wurin taron ne  don kare ra’ayinsa da na maigidansa ba na al’ummar da ya wakilta ba.  Don haka zabe ya fi nadi.