Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 1
Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka […]
Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu:
Ko shakka babu zabe ya fi nadi -Amina
Amina Muhammad Bello: A nawa ra’ayin babu yadda za a yi a hada yin zabe da kuma nadi. Zabe zai ba al’umma damar zabo wakilan da suka cancanta wadanda za su yi musu wakilci nagari, amma idan aka ce nadi za a yi ka ga kowane mutum za a iya tura shi don ya wakilci al’ummarsa walau ya cancanta ko bai cancanta ba, don haka zabe ya fi nadi, kuma babu abin da nadi zai haifar a wajen taron sai tattauna abin da gwamnati take son ji kawai ba abin da al’umma suke nema ba. Kuma da zabe za a yi, za a samu wakilcin mata da yawa ba maza kawai ba, don mata ma suna da rawar da za su taka.