Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 2
Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka […]
Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu:
Ba zai biya bukata ba – Abdullahi Shu’aibu
Abdullahi Shu’aibu: “Ni a ra’ayina, ina ganin kamata ya yi a bai wa jama’a dama su zabi mutanen da za su wakilce su a taron kasa, amma ba a nada su ba. Idan zabe aka yi mutune za su sami natsuwa a ransu, wato sun san za a yi musu wakilcin da ya dace. Amma idan nadi ne mutane ba za su san wanda aka nada musu ba, watakila ma a dauki mutanen da ba su damu da talakawa ba a kai su su wakilce su; kin ga a nan sai yadda ta yiwu ke nan. Kamata ya yi a bai wa kowace mazaba dama ta zabo wakili daga cikinta mutumin da ta san zai yi mata wakilci na gaskiya.”