Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 3

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka […]

Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 3
Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 3

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu:

Zabe ya dace a yi ba nadi ba – Muhamamd Sani

Muhammad Sani Ahmad: “Ina ganin idan aka yi zabe zai fi zama mafi alheri ga jama’a, domin za a fi samun zaman lafiya, domin kowace kabila ta san ita ta zabi mutanenta wadanda za su yi magana da yawunta a wannan taron kasa da za a yi, ba wai nada mata aka yi ba. Idan an duba dimokuradiyya muke yi, don haka kamata ya yi duk abin da za a yi wa jama’a a rika aiwatar da shi bisa ga tsari na zabe amma ba nadi ba. Ita kanta gwamnatin ai zabar ta aka yi, don haka a ba wa jama’a dama su zabi wakilansu.”