Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 4

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka […]

Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 4
Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 4

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu:

Nadi ba zai biya bukata ba – Bashari Direba

Malam Bashari Direba: “Ra’ayina dangane da taron kasa da ake kokarin gudanarwa, wanda a kan haka Gwamnatin Tarayya ke kokarin nada wakilan da za su halarta, wannan ba komai ba ne illa yunkurin cusa wasu bukatunsu da ke dauke da boyayyar manufa. In harAllah ake nufi da yin wannan taron kasa, to ai ba nada wakilan ya kamata a yi ba; a’a kamata ya yi a ba da dama ga al’umma su zabo wakilansu da suka amince da su amma ba wai a yi musu dauki-dora ba. Don haka a ganina, matukar ba dama aka bayar ga jama’ar kasa ba suka zabo mutanen da za su je don kare musu bukatunsu ba, to kuwa tamkar aikin kawai ne.”