Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 5

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka […]

Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 5
Ko nadin wakilan taron kasa maimakon zabe zai biya bukata? 5

Kamar yadda bayani ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta zartar da hukuncin cewa za a samar da wakilan da za su gudanar da taron kasa ta hanyar nadi ne maimakon zabe. Abin  tambaya a nan shi ne, ko hakan zai biya bukata kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan al’amarin kuma ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu:

Hakan danne ’yancin al’umma ne – Alhaji Ali

Shugaba Alhaji Ali Kunini: “A ra’ayina dangane da nada wakilan da za su halarci taron kasa da Gwamnatin Tarayya ta nemi gudanarwa, hakan wani kokari ne na yi wa al’ummar kasa karan tsaye da hana su ’yancinsu. Idan da gaskiya ake nufi da kiran wannan taro na kasa, da kamata ya yi a ba da dama ga al’ummar kasa su zabo wakilan da za su waklilce su, ba wai a yi musu nadi ba. Hakan tamkar karen tsaye ne ga hakkokin ’yan kasa. Don haka, wannan yunkuri na nada wakilai da bangaren Shugaban kasa ke shirin yi a taron da ba na dole ba, yin hakan ba daidai ba ne kuma tauye hakkin al’umma ne.”