Ko ni na tambaye ka kyautar fili a Abuja kar ka ba ni – Tinubu ga Wike

Tinubu ya bukaci shi ya mayar da hankali wajen farfaɗo da martabar Abuja

Ko ni na tambaye ka kyautar fili a Abuja kar ka ba ni – Tinubu ga Wike

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, da kada ya kuskura ya ba kowa kyautar fili a Abuja, ko da shi da kansa ne ya tambaya.

A maimakon haka, shugaban ya bukaci Wike ya dage wajen sake farfado da martabar Abuja a matsayin hamshakin birni abin alfahari.

Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi yayin bude taron shekara-shekara na Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) a Abuja, ranar Lahadi.

Shugaban ya kuma bayyana Wike a matsayin “Uban-dakin Abuja.”

“Ina so ka mayar da hankalinka wajen sake fargado da martabar Abuja. Ko Ni na nemi kyautar fili a wajensa, kada ka ba ni,” in ji Tinubu.

Wike, wanda dan jam’iyyar PDP ne dai na daya daga cikin ministoci 45 din da Tinubu ya rantsar a makon da ya gabata.